Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ƙauyukan Bauchi, Sun Tafka Mummunar Ta'asa

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ƙauyukan Bauchi, Sun Tafka Mummunar Ta'asa

Jihar Bauchi - 'Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Yadagungume da Limi a ranar Laraba a ƙaramar hukumar Ningi, inda suka kashe mutum uku kuma suka raunata mutum daya.

Jaridar The Punch ta ce wadanda aka kashe sun hada da Shuaibu Salihu (17), Ruwa Ali da aka fi sani da Mai Inji (45) da Sunusi Isah Burra.

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ƙauyukan Bauchi, Sun Yi Kisa Sun Raunata Mutane
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ƙauyukan Bauchi, Sun Yi Kisa Sun Raunata Mutane. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Wata majiya daga Ningi wadda ta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa wakilan majiyar Legit.ng cewa lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 12 na daren Laraba.

Ya ce yan bindigan sun fara kai hari ne Yadagungume suna harbi, suka tada hankalin mutane kafin daga baya suka afka kauyen Limi duk a yankin Burra a ƙaramar hukumar.

Majiyar ta ce:

Kara karanta wannan

Batanci Ga Annabin Rahma (SAW), Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

"Daga bayanan da muka samu, yan bindigan da ba a san adadinsun ba sun fara kai hari Yadagungume da bindiga kuma wani yaro ya fito yana ihu suka harbe shi.
"Yan bindigan sun sace mutum biyu amma dayansu ya tsere. Amma ba mu san abin da ya faru ba daga baya sun harbe dayan mutumin da suka sace. Wasu mata da ke hanyarsu ta zuwa gona da safe ne suka ga gawarsa.
"Daga baya sun kai hari kauyen Limi kuma suka kashe mutum daya kafin su tafi. Ba mu san abin da ya kai su garin ba don ba su ƙona ko gida ɗaya ba kuma ba su sace mutane ba illa biyun da daga baya suka kashe. Daya kuma yana asibiti ana masa magani saboda harbinsa da suka yi.
"An yi wa dukkan wadanda aka kashe jana'iza bisa tsarin koyarwar addinin musulunci."

Saurari karin bayani...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164