Bamu bada izinin kara farashin wutan lantarki ba tukun, Hukumar NERC
- Kuma dai, gwamnatin tarayya ta ce ba ta shirin kara farashin wutan lantarki a kimanin jihohi ashirin da uku
- Shugaban hukumar NERC yace duk wanda ya ga an yi masa karin kudi ya gabatar da hujjan haka
- Wannan ya biyo bayan lalacewa wutan lantarkin da aka yi fama tsohon watanni biyu a fadin tarayya
Abuja - Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC ta bayyana cewa bata bada izinin kara farashin wuta ba tukunna.
Shugaban hukumar, Garba Sanusi, yayin hira da manema labarai ranar Juma'a ya karyata rahotannin da ke kafafen yada labarai cewa za'a yi karin farashi, rahoton ChannelsTV.
Yace duk wanda ya ga an kara masa kudin wuta ya shigar da kara da hujja.
A cewarsa:
"A madadin hukumar NERC, ina mai bayyana cewa kawo yau (Juma'a), bamu bada izinin kara farashin wuta ga kamfanonin rarraba wuta ba kuma babu hujja dake nuna an kara."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Idan ka ga farashin lantarkin da ka saya ta karu cikin makonni uku da suka gabata, ka kawo hujja."
Ya kara da cewa bayanin dake shafin yanar gizonsu na Disamban 2021 ne.
Barna a hasumiyar rarrabe wutar lantarki ce ta kai ga lalacewar wutar Ƙasa, FG
Ma'aikatar wutar lantarki ta tarayya a ranar Asabar ta ce lalacewar wutar lantarkin kasar nan ya biyo bayan barna da ake yi wa kasar a hasumiyar rarrabe wutar lantarkinta.
TheCable ta ruwaito cewa, wutar Najeriya ta lalace a ranar Juma'a, karo na uku a cikin makonni kadan, lamarin da ya jefa wasu jihohin kasar cikin matsalar wutar lantarki.
Da farko da, ma'aikatar wutar lantarkin ta ce tana bincikar dalilin lalacewar wutar kasar.
Asali: Legit.ng