A Umurci Tsohuwar Matata Ta Dawo Min Da Sarƙan Lu’u-lu’un Da Ba Ta, Magidanci Ya Roƙi Kotun Shari'a
- Wani dan kasuwa, Mustapha Baba ya bayyana wa wata kotun musulunci da ke Jihar Kaduna sharadin da matarsa za ta cika don ya sake ta kamar yadda ta bukata
- A cewarsa, in har ta dawo masa da sarkar lu’u-lu’un da ya bata, take a wurin zai sahhale mata igiyar aurensa da ke kanta
- Kamar yadda matar, Amina Sani ta bayyana wa kotu, tana so a raba aurensu ne don kada ta saba wa Ubangiji ta hanyar kin yi wa mijinta biyayya
Kaduna - Mustapha Baba, wani dan kasuwa ya roki wata kotun musulunci da ke Jihar Kaduna ta umarci tsohuwar matarsa, Amina Sani, ta dawo masa da sarkar lu’u-lu’un da ya bata.
A cewarsa, hakan ne kadai sharadin da za ta cika in har tana son a raba aurensu, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda NAN ta ruwaito, Baba, wanda mazaunin garin Kaduna ne, ta lauyansa, Ahmad Ibrahim ya sanar da kotu cewa wanda ya ke karewa ya na da tarin bukatu.
Tun farko Amina ce ta bayyana gaban kotu ta na bukatar a raba aurenta da mijinta don gudun ta saba wa Ubangiji don ba za ta iya yi masa biyayyar aure ba.
A cewarta:
“Ba zan biya shi sadakin N50,000 din da ya biya don aure na ba.”
Alkalin ya dage sauraron karar
Daga bisani, lauyan mai kara, M. K Mustapha ya nemi kotu da ta dage sauraron karar don a samu damar yin bincike mai yawa akan lamarin da kuma ganin yiwuwar shiryawar miji da matar.
Alkalin, Malam Murtala Nasir bayan sauraron duk bangarorin guda biyu, ya bayyana cewa a musulunci, in har mace ta na bukatar a raba aurensu da mijinta, sai ta biya shi sadakin da ya bayar don aurenta.
Daga nan Nasir ya dage sauraron karar.
Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki
A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.
Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.
Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.
Asali: Legit.ng