Kungiyar ta'addancin Ansaru na diban ma'aikata a Kaduna, suna raba goron Sallah

Kungiyar ta'addancin Ansaru na diban ma'aikata a Kaduna, suna raba goron Sallah

  • Tsagin Boko Haram, kungiyar ta'addanci ta Ansaru ta fara diban ma'aikata a jihar Kaduna inda take ta raba takardu da goron sallah
  • Lamarin na faruwa ne a wasu kauyukan karamar hukumar Birnin Gwari inda har wasan babur mai kayatarwa suka yi wa jama'a da sallah
  • A takardar da suka raba, sun sanar da cewa su ba Boko Haram bane, masu jihadi ne kuma sunnar Annabi suke bi da magabatan farko

Kaduna - Mambobin kungiyar ta'addanci ta Ansaru sun fara diban aiki inda suka daukan mazauna yankin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, jaridar Daily Trust ta tattaro.

Ansaru, wani sashin kungiyar ta'addanci ne na Boko Haram kuma sun kasance suna cin karensu babu babbaka a kauyukan Birnin Gwari na tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗalibar Sokoto

Kungiyar ta'addancin Ansaru na diban ma'aikata a Kaduna, suna raba goron Sallah
Kungiyar ta'addancin Ansaru na diban ma'aikata a Kaduna, suna raba goron Sallah. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A ranar Laraba, Daily Trust ta tattaro cewa, mambobin kungiyar sun zagaye kauyukan Damari, Farin Ruwa, Kwasa Kwasa, Kuyello, Gobirawa har da Tabanni, Kutemeshi da Kazage duk a cikin dabarunsu na daukar jama'a aiki wanda suka fake da shagalin sallah suke.

Wasu mazauna kauyukan da suka zanta da manema labarai sun ce 'yan ta'addan sun rarraba goron Sallah da ya hada da biskit, sun yi wasan mashin wanda ya kayatar da jama'a kuma sun raba takardu da sauran kayayyaki duk daga kungiyar.

Birnin Gwari tana yankin tsakiyar jihar Kaduna ne kuma 'yan ta'adda sun samu damara ratsa ta inda kudanci da gabashinta ne suka fi shan wuyar.

Abinda takardar da suka raba ta kunsa

Takardar mai shafi biyar mai taken: "Mu ba Boko Haram bane, Ansaru ne" mambobin kungiyar sun dinga raba ta a kokarinsu na jan hankalin mazauna yankin su shiga kungiyarsu.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Takardar an rubuta ne a tsarin tambayoyi da amsoshinsu. Ta ce "Sunanmu Jama’atul Ansaril Muslimina Fi Biladis Sudan.”

Takardar ta kara da ikirarin cewa abinda kungiyar ta fito yi shi ne jihadi inda ta kara da cewa bambancinta da sauran kungiyoyin jihadi shi ne suna bin sunnar Annabi ne da magabata.

Sai dai masana a harkar tsaro sun yi watsi da wannan ikirarin inda suka ce gwamnati, malamai da sarakuna dole su tashi tsaye gudun abinda ya faru a yankin arewa maso gabas.

Sun ce miyagun mutane masu tsawwalawa a addini sun saba amfani da tausasan kalamai wurin yaudarar mutane har su mika wuya kafin su nuna inda suka dosa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng