Shugaban majalisar dinkin Duniya ya fadawa Shugaba Buhari sirrin yakar ‘Yan ta’adda
- Shugaban majalisar dinkin Duniya ya kawo wata ziyarar gani da ido zuwa yankin Arewacin Najeriya
- Mista Antonio Guterres ya hadu da Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa a kan batun rashin tsaro
- Guterres ya kawo shawarar hanyar da za a bi domin a wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali
Abuja - Shugaban majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres ya nuna muhimmancin komawa tushe wajen yakar ta’addancin da ke addabar Najeriya yau.
Jaridar Daily Trust ta ce Antonio Guterres ya yi wannan bayani ne da yake amsa tambaya daga wajen menama labarai a fadar Aso Villa da ke birnin Abuja.
Guterres ya yi zama da Mai girma Muhammadu Buhari, bayan nan kuma ya hadu da ‘yan jarida.
Shugaban majalisar dinkin Duniyan ya yi bayanin kokarin da su keyi wajen taimakawa gwamnatocin Afrika wajen murkushe masu tada kafar baya.
Jawabin Mista Antonio Guterres
“Abu ne mai sauki, na gani a Borno. Idan ka yaki ta’addanci da karfin bindiga zalla, ‘yan ta’adda za su dawo su yake ka.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Amma idan aka yaki ‘yan ta’adda da karfin bindiga da kuma bibiyar tushen ta’addancin, ba za su samu damar cigaba ba.”
“Ina tunanin Mao Tse Tung ne yake cewa tada zaune-tsaye yana yawo ne tamkar yadda kifi yake iwo a cikin ruwa.”
“Idan mutane su ka iya kare su, su ka yarda da gwamnatocinsu, kuma aka kawo tsare-tsare, za a iya magance ta’addanci.”
- Antonio Guterres
A yafewa tsofaffin 'yan ta'adda
Daga cikin tsare-tsaren da za su kawo zaman lafiya a cewar Guterres akwai karbar tsofaffin ‘yan ta’addan da suka ajiye makamai, a sama masu sabuwar rayuwa.
Guterres ya ce dole ne a tabbatarwa wadanda rikicin ta’addanci ya rutsa da su cewa su na da makoma. Vanguard ta tabbatar da haka a wani rahoto da aka fitar.
Zuwan shugaban majalisar dinkin Duniyan Najeriya ya taimaka masa wajen sanin asalin mawuyacin halin da ‘yan gudun hijira da sauran mutane ke ciki.
Zulum zai yi takara
An ji cewa an samu wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suka tarawa Babagana Umara Zulum kyautar N50m.
Wadannan kungiyoyi sun ba Gwamna Zulum gudumuwa ne saboda jin dadin aikin da ya ke yi a jihar Borno
Asali: Legit.ng