Da Dumi-Dumi: Nakiya ta kara fashewa da mutane a jihar Imo, mutum biyu sun rasu
- Wani abun fashewa da ya ƙara tashi kusa da Kamfanin Man Fetur ya yi ajalin mutum biyu har lahira a jihar Imo
- Bayanai sun nuna cewa mutum biyun na kan hanyar da ta nufi kamfanin lokacin da abun ya fashe suka mutu nan take
- Mako biyu da suka gabata, akalla mutane 110 suka rasa rayukan su lokacin da wata wuta ta tashi a matatar mai ta haram duk a Imo
Imo - Mutum biyu sun mutu yayin da wani abun fashewa da ake zaton Bam ne ya tashi da wasu gine-gine kusa da kamfanin mai Addax Oil a Izombe, ƙaramar hukumar Oguta, jihar Imo ranar Laraba.
Wata majiya ta bayyana cewa waɗan da lamarin ya shafa sun nufi hanyar da zata kai su kamfanin Man na Addax Oil kafin fashewar nakiyar.
Jaridar Ledearship ta rahoto cewa mutanen biyu sun rasa rayuwarsu nan take a wurin da abun ya fashe.
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Imo, Michael Abattam, ya tabbatar da aukwar lamarin, inda ya ce tuni hukumarsu ta tura jami'an tsaro.
Abattam ya bayyana cewa hukumar yan sanda ta aike da dakarun warware Bam zuwa wurin da abun ya auku domin daƙile sake faruwar haka nan gaba.
Vanguard ta rahoto ya ce:
"Mun samu rahoton abun da ya faru kuma tuni aka aike da dakarun cire Bam zuwa wurin domin dakile sake faruwar haka nan gaba, yayin da ake cigaba da bincike."
Wannan ba shi ne karon farko ba
Idan baku mance ba mako biyu da suka gabata. aƙalla mutane 110 suka mutu sakamakon wata fashewa da aka rasa gane musabbabinta a haramtacciyar matatar Man Fetur dake Abaezi ƙaramar hukumar Ohaji-Egbema duk a Imo.
Har yanzun dai babu wani cikakken bayani kan yadda mutanen da abun ya shafa suke tattare da abun fashewa.
A wani labarin na daban kuma Gwamnan APC a Arewa da wani Ministan Buhari sun ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023
Gwamnan jihar Jigawa a arewacin Najeriya, Abubakar Badaru, ya sayi Fom din tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.
Ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya bi sahun gwamnan ya tara masoya ya bayyana kudirinsa idan ya zama shugaban kasa.
Asali: Legit.ng