Ana binciken Hadiman Abubakar Malami kan ‘karbar kudi’ domin yi wa barayi afuwa

Ana binciken Hadiman Abubakar Malami kan ‘karbar kudi’ domin yi wa barayi afuwa

  • Hukumar EFCC ta na binciken yadda gwamnatin tarayya ta yi wa wasu manyan masu laifi afuwa
  • Zargin da ake yi shi ne, ma’aikatan shari’a sun karbi kudi domin a yafewa wasu marasa gaskiya
  • Cikin mutum kusan 160 da aka yi wa afuwa, akwai wadanda aka yi mamakin yadda sunansu ya fito

Abuja - Hukumar EFCC ta tsare wasu daga cikin manyan jami’an ma’aikatar shari’a, ta yi masu tambayoyi a game da batun mutanen da aka yi wa afuwa.

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto na musamman da ya bayyana cewa ana zargin ma’aikatan da rashin gaskiya wajen tattara wadanda aka yafewa laifinsu.

Wata majiya ta shaida cewa Hadiman Ministan shari’a, Abubakar Malami da ke da alhakin tattara sunayen mutanen da za ayi wa afuwa, sun shiga hannun EFCC.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

TheCable ta bi diddikin wadanda aka yi afuwar, ta gano a jerin akwai manyan masu laifin da suka hada da satar kudin al'umma da yunkurin yin juyin mulki.

“Daga cikin abin da ya bada mamaki shi ne yadda aka cusa sunan Atuche a sunayen da aka gabatarwa majalisar koli na kasa.”
“Akwai sunayen mutanen da suka jawo hukumar EFCC ta ke zargin lamarin, har ta kai ta fara kiran wasu domin ta yi bincike.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Majiyar ma'aikatar shari'a

AGF Abubakar Malami
Ministan shari'a, Abubakar Malami SAN
Asali: UGC

Lamarin Francis Atuche

Alal misali a shekarar 2021 kotu ta samu Francis Atuche da laifin satar Naira biliyan 25.7. Wannan ya sa aka yanke masa daurin shekaru 12 a gidan kurkuku.

Ko shekara daya Atuche bai yi a gidan yari ba, sai ga shi ana neman fito da shi daga magakarma. Ana kai sunansa gaban majalisar koli, aka yi fatali da shi.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Wadanda ake bincike

Darekta a harkar kula da manyan laifuffuka da kawo gyara a ma’aikatar shari’a, Leticia Ayoola-Daniels ta na cikin wadanda EFCC su ke bincike a yanzu.

Rahoton ya nuna wasu wadanda yanzu su ke hannu sun gagara cin jarrabawar da ake yi masu. Su na kafa hujja da cewa su na fama da matsalar hawan jini.

An yafewa tsofaffin gwamnoni

Kwanakin baya aka ji cewa gwamnatin Najeriya ta yi wa wasu mutum sama da 160 afuwar laifin da suka yi. A cikinsu akwai wasu tsofaffin gwamnoni biyu.

Majalisar koli ta yafewa duka wadanda shugaba Muhammadu Buhari ya nemi ayi masu afiyar illa tsohon bankin nan na PHB, Francis Atuche da wasu mutum.

Tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan Filato, Joshua Dariye, su na cikin wadanda aka ceto da sunan tsufa da kuma rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng