Zagayen ranar Qudus: 'Yan shi'a sun musanta kona ofishin 'yan sanda a Zaria

Zagayen ranar Qudus: 'Yan shi'a sun musanta kona ofishin 'yan sanda a Zaria

  • Kungiyar mabiya Shi'a sun nesanta kansu daga kona ofishin yan sanda a yayin da suke gudanar da zagayen ranar Qudus a garin Zaria
  • Kungiyar ta kalubalanci jama'a da su garzaya ofishin yan sanda da ke kasuwar Mata don tabbatar da ikirarinsu
  • Sun kuma zargi yan sanda da kwamushe masu mambobinsu fiye da guda 70 tare da hana su samun kulawar likitoci duk da cewar suna mawuyacin hali

Kaduna - Kungiyar Musulmai mabiya Shia sun yi watsi da zargin cewa mambobinsu sun cinnawa wani ofishin yan sanda wuta a yayin da suke gudanar da zagayen ranar Qudus a garin Zaria.

Wakilin shugaban kungiyar na kasa a Zaria, Mallam Abdulhamid Bello, wanda ya karyata zargin a wani taron manema labarai a Zaria, ya ce ana iya zuwa ofishin yan sanda na Kasuwar Mata sannan a duba a gani ko an kona sa, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Zagayen ranar Qudus: 'Yan shi'a sun musanta kona ofishin 'yan sanda a Zaria
Zagayen ranar Qudus: 'Yan shi'a sun musanta kona ofishin 'yan sanda a Zaria Hoto: Original
Asali: UGC

Ya ce:

“An farmaki tattakin wannan shekarar a Zaria ta hanyar fakewa da cewar mambobin kungiyar sun cinna wuta a ofishin yan sandan Sabon gari da wata mota.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Yana cikin tarihi cewa sama da shekaru 40 muna tattakinmu karkashin shugabancin Sheikh Ibrahim Zakzaky cikin lumana har sai lokacin da jami’an tsaro suka farmake mu.”

Mallam Bello ya bayyana cewa a yanzu haka akwai mambobinsu guda takwas kwance a asibiti sakamakon raunukan harbi da suka ji.

Ya kuma ce an garkame sama da mutum 70 da suka hada da mata da yara wadanda suke rai a hannun Allah a ofishin yan sanda ba tare da basu kulawar da suke bukata ba.

Rahoton ya nakalto inda yake ci gaba da cewa:

“Bamu da hannu a kona motar da ofishin yan sandan Sabon gari.”
“Don haka, muna kira da a gaggauta sakin dukkanin wadanda ke tsare a hannun yan sanda. Hakazalika, muna son amfani da wannan damar wajen kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta sakin takardun tafiyar Sheikh Zakzaky da matarsa Malama Zeena domin su samu damar duba lafiyarsu.”

Kara karanta wannan

Sokoto: An kama wadanda suka kashe dalibar da ake zargin ta zagi Annabi

'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria

A gefe guda, mun kawo a baya cewa an yi arangama tsakanin Musulmi mabiya Shi'a da jami'an tsaro a garin Zaria.

'Yan shi'an sun fito tattaki da zanga-zanga inda bayanan da Legit.ng ta tattaro suka bayyana cewa sun fara tun daga Masallacin 'yan kaji da ke cikin kasuwar Sabon Gari a Zaria.

Ganau ba jiyau ba sun tabbatarwa da Legit.ng yadda 'yan Shi'an suka gangara a kasa suna tattakinsu tare da toshe hannu daya na tagwayen titin da ke PZ a Zaria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng