Da dumi-dumi: Ba'a ga jinjirin wata ba a Najeriya, za'a cika 30 ras: Sarkin Musulmi

Da dumi-dumi: Ba'a ga jinjirin wata ba a Najeriya, za'a cika 30 ras: Sarkin Musulmi

  • Bayan faduwar rana, Sarkin Musulmi ya yi sanarwa game da lamarin ganin watar Shawwal
  • A jihohin akalla bakwai; Misau jihar Bauchi, Sokoto, Kaduna, Lagos, Ilorin, Abuja da Abeokuta, ba'a ga wata ba
  • An yi umurni Musulmai a fadin Najeriya zasu karashe azuminsu na Ramadan ranar Lahadi 30 ga Afrilu

Abuja - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad III ya sanar da cewa bayan duban wata da aka yi a fadin tarayya, ba'a ga jinjirin watan Shawwal a Najeriya ba.

Sarkin ya ce sakamakon haka gobe za'a tashi da azumi don watan Ramadan ya cika Talatin (30) kuma ayi ranar Litinin 2 ga watan Mayu, 2022.

Ga jawabin Sarki:

Da dumi-dumi: Ba'a ga jinjirin wata ba a Najeriya, za'a cika 30 ras: Sarkin Musulmi
Da dumi-dumi: Ba'a ga jinjirin wata ba a Najeriya, za'a cika 30 ras: Sarkin Musulmi
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wasu Musulmai sun saba Umarnin Sarkin Musulmi, sun gudanar da Sallar idi a Sokoto

Dazu mun kawo muku cewa kwamitin duba wata ta majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya ta bayyana cewa kawo karfe 7:35 na daren Asabar an samu rahotanni daga jihohi bakwai.

Dukkan rahotannin sun nuna cewa ba'a ga jinjirin wata ba.

Wadannan jihohi sun hada da Misau jihar Bauchi, Sokoto, Kaduna, Lagos, Ilorin, Abuja da Abeokuta.

Jawabin kwamitin yace:

"Kawo yanzu rahoton da muka samu daga Misau, Sokoto, Kaduna, Lagos, Ilorin, Abuja da Abeokuta ba'a ga wata ba."
"A wasu yankunan akwai haske a sama amma ba'a ga watan ba."

Watan Ramadan zai cika kwana 30 a Nigeria da Kasar Saudi Arabia

Wani masani, Adamu Ya'u ya yi bayanin cewa watan Ramadan zai cika Kwana 30 a Nigeria da Kasar Saudi Arabia

A bayanan da marubuci kuma masanin ilmin sararin samaniya yayi, ya ce Za'a Samu kisfewar Wata, a cikin Watan Shawwal.

Kara karanta wannan

Dan Majalisa Da Aka Kama Yana Kallon Fim Ɗin Batsa a Wayansa Yayin Zaman Majalisa Ya Yi Murabus

Yace:

Na Tabbata Saudi_Arabia Ba za su ga Wata a ranar Duban Fari ba, kuma babu wanda zai yi musu Tawaye.

Amma mu a Nigeria kusan Abinda ya faru a wanchan shekarar ina tunanin zai sake faruwa, kamar yadda wanchan shekarar muka tabbatar Babu Wata a Sama Bayan Faduwar Rana a ranar Duban Fari, amma a haka aka samu wasu wai Sun ga Wata.

Kuma wasu da basu san meye ilimi akan wata ba suna ta sukar Mai Alfarma Sarkin Musulmi akan wai anga wata yaki tabbatar wa, Daman ai ba zai amince ba, saboda yanzu ilimi yazo ba yadda za'a yi amfani da cewa anga wata Alhali babu wata a ranar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng