Wata za ta riga rana fadi ranar Asabar amma duk da haka a fita duban wata, kwamitin duban wata
2 - tsawon mintuna
- Kwamitin dubar wata ya yi bayanin yadda tsayuwar jinjirin Watar Shawwal (1443AH) zata Kasance cikin ikon Allah
- Istinbadi daga jawabin da ta fitar, da alamun watan Ramadan zai cika Kwana 30 a Nigeria
- Amma bisa koyarwan addinin Musulunci, an ce a fita duban wata gobe Asabar bayan faduwar rana
Kwamitin dubar wata dake karkashin kwamitin koli na lamuran addinin Musulunci a Najeriya ya yi bayani game da yadda tsayuwar jinjirin Watar Shawwal (1443AH) zata Kasance cikin ikon Allah.
A jawabin da ya fitar ranar Juma'a a shafin Facebook, kwamitin yace ana sa ran haihuwar sabuwar watar misalin karfe 9:28 na dare kuma watar za ta fadi kafin rana kuma ba zai ganu a sararin samaniya ba.
Yace:
"Gobe Asabar ne 30 ga Afrilu 2022, wanda yayi daidai da 29 ga Ramadan 1443(H) kuma ranar fara neman watar Shawwal 1443(H)."
"Ana hasashen haihuwar jinjinrin wata a Najeriya bayan faduwar ranar ranar Asabar 30 ga Afrilu misalin karfe 9:28 na dare. Hakan na nuni da cewa wata za ta riga rana fadi saboda haka ba zata ganu a sama ba bayan faduwar rana."
"Bisa koyarwar Sunnah, kwamitin duban wata na kira ga al'umma su nemi wata wadannan kwanakin biyu sannan su turo mana abinda suka gani."
Watan Ramadan zai cika kwana 30 a Nigeria da Kasar Saudi Arabia
Wani masani, Adamu Ya'u Dan America ya yi bayanin cewa watan Ramadan zai cika Kwana 30 a Nigeria da Kasar Saudi Arabia.
A bayanan da marubuci kuma masanin ilmin sararin samaniya yayi, ya ce Za'a Samu kisfewar Wata, a cikin Watan Shawwal.
Yace:
Idan baku manta tun shekaran da ya wuce lokacin da muka kammala Azumi 30 na sanar da ku cewa idan Allah ya kawo mu Wannan shekara, shi ma akwai wani Dama na sake samun Azumi 30 idan har an dauki Azumi a ranar Asabar (02/04/2022).
Dukkan mu Nigeria da Saudiyya idan Allah ya kaimu ranar 29 ga Watan Ramadan, Wata zai riga Rana Faduwa.
Asali: Legit.ng
Tags: