Kar kuce zaku rama: Kwamandan Civil Defence ya yi gargadi kan harin da MOPOL suka kai musu
- Shugaban hukumar Sibil Defens ya gargadi jami'ansa kada suce zasu kaiwa yan sandan MOPOL hari kan abinda ya faru ranar Litnin
- Jami'an hukumar Mobile Police MOPOL sun kai wa jami'an Civil Defense hari har ofishinsu a Owerri
- Kwamandan yace ramuwar gayya ba itace mafita ba, su yi hakuri za'a shawo kan lamarin
Abuja - Kwamandan Janar na hukumar NSCDC, Dr Ahmed Abubakar Audi, ya gargadi jami'ansa kada su sake su ce zasu rama abinda jami'an yan sanda suka yi musu a jihar Imo.
Legit ta kawo muku cewa ranar Litnin jami'an yan sanda sun kai hari ofishin NSCDC kuma suka yiwa kwamandan zindir, suka kashe dogarinsa.
Martani kan lamarin ranar Talata, Shugaban hukumar NSCDC na kasa ya yi kira ga jami'ansa su kwantar da hankulansa kuma kada su dau doka a hannu, rahoton Vanguard.
Kashe-kashen Kanam: Yadda gwamna Lalong ya yi watsi da gargadin da nayi masa – Shugaban karamar hukuma
Diraktan yada labaran hukumar, DCC Olusola Odumosu, a jawabin da ya fitar ya ruwaito Kwamanda Janar na NSCDC cewa wajibi hukumomin tsaro su hada kai da juna don samarwa kasa tsaro.
A cewarsa, ramuwar gayya ba ita ce mafita ba, saboda ba a gyara kuskure da wani kuskuren.
Yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Akwai hanyoyi mafi dacewa da za'a iya sulhunta matsalar ba tare da fadace-fadace ba ko kaiwa ofishohin juna hari."
Me takamammen abinda ya faru tsakanin yan sanda da Civil Defence
Rikici ya barke tsakanin yan sanda da jami'an NSCDC watau Sibil defense sakamakon rashin jituwan da ya wakana tsakanin jami'an hukumomin tsaron biyu a jihar Imo.
Leadership ta ruwaito cewa yan sandan sun kai farmaki hedkwatar NSCDC dake Owerri, ranar Litinin kuma suka yiwa kwamandansu zindir kuma suka kashe dogarinsa.
Rahoton ya kara da cewa rikicin ya fara lokacin da wani dan sanda sanye da kayan gida ya tare hanya, ya hana kwamandan NSCDC wucewa yayinda yake hanyar komawa Owerri daga Abacheke, inda matatar man sata tayi gobara.
Wani jami'an Sibil Defence mai suna Ikechukwu yace:
"Lokacin da dogaran kwamanda suka cewa dan sanda ya tashi daga hanya, ya ki. Sai ya kira sauran abokansa yan sanda daga hedkwatar yan sanda kuma ya bisu ofishinsu.
"Yayinda suka kai ofishin NSCDC, dan sandan ya sake tare hanya ya fito da bindigarsa yana ikirarin cewa shi dan sanda ne. Kawai sai jami'an NSCDC suka zagayeshi suka kwace bindigar kuma suka garkame shi."
Wani jami'in hukumar wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace,
"Bayan an sakeshi, sai ya dawo da rundunar MOPOL kuma suka shiga dukan jamianmu suka lalata kayan ofishinmu."
Yayinda aka fara harbe-harben bindiga, sa ya kwamandan ya fito sulhunta lamarin, amma yan sandan suka yi masa lilis kuma suka cire masa riga sukayi awon gaba da shi.
Asali: Legit.ng