Ba zan yi murabus a matsayin Minista ba, Karamin ministan Ilmi da ya sayi Fom din takara

Ba zan yi murabus a matsayin Minista ba, Karamin ministan Ilmi da ya sayi Fom din takara

  • Emeka Nwajiuba ya lashi takobin cewa ba zai yi murabus daga matsayin Ministan ilmin karkashin mulkin Buhari ba
  • Ya ce zai cigaba daga inda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta tsaya idan ya samu nasara
  • Nwajiuba yace kundin tsarin mulki ta bashi daman cigaba da zaman kan kujerarsa har sai ana saura kwanaki 30 zabe
  • Ministan ya yi kira da kungiyar Malaman jami'o'in Najeriya ASUU su koma aji don karantar da dalibai

Abuja - Karamin Ministan Ilmi, Emeka Nwajiuba, ya bayyana cewa ba zai yi murabus daga kujerarsa ba don ya ayyana niyyar takara kujeran shugaban kasa a 2023.

Jam'iyyar APC za ta gudanar da zaben fidda gwaninta ranar 29 da 30 ga Mayu, 2023.

Nwajiuba ya ce ya amince ya yi takara kujeran ne don zama shugaban Najeriya wanda zai cigaba daga inda shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

Ya ce ba zai yi murabus ba sai ana sauran kwanaki 30 zabe kamar da kundin tsarin mulkin Najeriya ta tanada.

A cewarsa,

"Kundin tsarin mulkin Najeriya ce ta tsara yadda minista ko kowani mutum zai yi murabus."
"An bamu daman takara a zabe idan muna so. An bukaci muyi murabus ana sauran kwanaki 30 zabe. Wannan shine doka. Kowa na iya fadin ra'ayinsa."

Ba zan yi murabus a matsayin Minista ba, Karamin ministan Ilmi da ya sayi Fom din takara
Ba zan yi murabus a matsayin Minista ba, Karamin ministan Ilmi da ya sayi Fom din takara
Asali: Facebook

Kungiyar Project Nigeria ya sayawa Emeka Nwajiuba, Fom din takaran shugaban kasa N100m

Karamin Ministan Ilmi, Hanarabul ChukwuEmeka Nwajiuba, ya sayi Fom din takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC N100m.

Nwajiuba ya sayi Fom din ne a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu, a hedkwatar uwar jam'iyyar APC dake birnin tarayya Abuja.

Kungiyar Project Nigerian, ta wasu yan Najeriya ne suka hada masa kudi milyan dari kuma suka saya masa Fam din.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara kujerar yankinsu

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng