Hotuna: Asiwaju Bola Tinubu ya shiga jerin yan Najeriya da suka garzaya aikin Umrah
Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress APC kuma mai niyyar takaran kujeran shugaban kasa a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya tafi kasa mai tsarki don gabatar Ibadar Umrah.
Tinubu, a hotunan da hadimansa suka saki ya gabatar da ibadar ne tare da makusantarsa da abokan siyasa.
Daga cikinsu akwai tsohon shugaban hukumar EFCC kuma tsohon dan takaran kujeran gwamnan Adamawa, Alhaji Nuhu Ribadu.
Wannan ya biyo bayan tafiyar gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, aikin Umrah da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
Kalli hotunan:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2023: Yahaya Bello Ya Shige Gaban Su Tinubu, Ya Fara Biyan N100m Lakadan Kuɗin Fom Ɗin Takara
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi, zai karbi fom din takarar zabensa a ranar Laraba, rahoton Daily Trust.
Gwamnan ya biya Naira miliyan 100 a safiyar ranar Talata, hakan na nufin shine mutum na farko da a hukumance ya siya fom din takarar shugaban kasa na 2023 a jam'iyyar, a cewar sanarwar da Direktan Watsa Labaran Yahaya Bello Kamfen, Yemi Kolapo ya ce.
Gwamnan ya ayyana niyyarsa na neman takarar shugabancin kasar a filin Eagle Square da ke Abuja a ranar 2 ga watan Afrilun 2022.
Asali: Legit.ng