Yanzu-yanzu: Sarkin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya rigamu gidan gaskiya

Yanzu-yanzu: Sarkin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya rigamu gidan gaskiya

  • Daya daga cikin manyan Sarakunan kasar Yarabawa a Najeriya, Alaafin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya rasu
  • An ruwaito cewa Oba Lamidi Adeyemi ya yi jinya a asibitin jami'ar ABOUAD dake birnin Ado Ekiti
  • Oba Adeyemi ya shahara da motsa jiki, kyauta da dattaku kuma tsohon dan dambe ne

Oyo Alaafin - Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa Allah ya yiwa Sarkin Oyo, babbar Sarki a kasar Yarbawa, Oba Lamidi Adeyemi, rasuwa.

Oba Adeyemi ya mutu ne da yammacin Juma'a a Asibitin koyarwa jami'ar Afe Babalola dake Ado Ekiti, rahoton Premium Times.

Cikin dare aka gaggauta kai gawarsa jihar Oyo domin fara shirin jana'izarsa.

Adeyemi ya mutu yana mai shekaru 83 bayan kwashe shekaru 52 kan mulki.

Sarkin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi
Yanzu-yanzu: Sarkin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya rigamu gidan gaskiya Hoto: Oyo State Government
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Maziyarta da maniyyata 51 sun yi hadarin mota a Madina, mutum 8 sun kwanta dama

Ana sauraron gwamnna jihar Oyo, Seyi Makinde, ya sanar da mutuwar Sarkin bayan samun labari daga wajen Bashorun of Oyo, Yusuf Akinade, wanda shi zai jagoranci masarautar kafin a nada sabon Oba.

Sarkin ya kwana biyu yana rashin lafiya kuma ana shirin kai shi kasar waje jinya.

Wata majiya dake da masaniya kan lamarin ta ce tuni an shirya tikiti da bizan Sarkin da wasu cikin matansa.

Mutuwarsa na zuwa bayan mutuwan manyan Sarakunan jihar biyu - Olubadan Ibadan, Saliu Adetunji, da Soun of Ogbomoso, Jimoh Oyewumi

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: