Mu muka kai harin Bam mashaya a jihar Taraba, Kungiyar ISWAP
- Bayan kwana biyu da harin, yan ta'addan ISWAP sun bayyana cewa su suka dasa Bam a jihar Taraba
- Cikin kwanaki biyu a jere yanzu an kai harin Bam mashaya a yankin Arewa maso gabashin Najeriya
- Wasu daga cikin wadanda suka jikkata sakamakon harin Bam da aka kai Taraba sun rasa rayukansu
Kungiyar yan ta'addan Islamic State in West Africa Province (ISWAP) sun dau alhakin harin Bam da aka kai kasuwar sayar da kayan maye a jihar Taraba, rahoton AlJazeera.
Kungiyar tace Bam din da ta dasa ya hallaka ko jikkata akalla mutum 30.
A cewar AlJazeera, kungiyar ISWAP a jawabin da ta fitar da daren Laraba a shafinta na Telegram tace wadanda suka dasa Bam din "Sojojin Khilafa a Najeriya."
Jawabin yace , ISWAP tace ta kashe kafirai kuma tana farin ciki saboda an tarwatsa mashayar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Harin Bam a gidan giya a Taraba: Kawo yanzu mutum 16 sun mutu
Adadin wadanda suka mutu a harin Bam din da aka kai gidan mashaya a Iware, karamar hukumar Ardo-Kola ya kai 16, masu idanuwan shaida sun bayyana.
Amma kakakin hukumar yan sandan jihar Taraba, DSP Abdulahi Usman, yace mutum shida kadai suka san sun mutu.
Punch ta ruwaito cewa mutane daban-daban wanda suka hada da James Audu, Mrs. Abaagu Esther da Musa David sun bayyana cewa mutum 10 da aka kai asibiti sun mutu kawo safiyar Laraba.
Wannan bakon abu ne a jihar Taraba
Arewa maso gabashin Najeriya na fama da yan ta'adda masu tada kayar baya tsawon shekaru goma yanzu, amma jihar Taraba, bata taba fuskantar hari irin wannan ba.
Wannan shine karo na farko da aka kai harin Bam jihar Taraba.
Asali: Legit.ng