Da dumi: Yan Boko Haram sun kai hari mashaya a Yobe, sun kashe 9, sun kona Kwalejin Fasaha
- Yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun kai hari karamar hukumar Geidam da daren Laraba a Yobe
- Ana fargaban akalla mutum tara sun rasa rayukansu a harin da yan ta'addan suka kai mashaya
- Wannan ya biyo bayan harin Bam da yan ta'adda suka kai mashaya a jihar Taraba
Yobe - Wasu yan ta'adda masu tada kayar baya da ake zargin yan kungiyar ISWAP ne sun kai hari ranar Laraba karamar hukumar Geidam a jihar Yobe kuma suka kona makarantar fasaha kurmus.
Vanguard ta ruwaito cewa cikin wadanda harin ya shafa akwai yan biyu.
Daya ya mutu kai tsaye, yayinda aka garzaya da dayan asibiti don jinya.
Harin ya auku ne misalin karfe 9 na dare.
Majiyoyi sun bayyana cewa yan ta'addan sun shiga garin ne da kafa kuma suka bude wuta kuma suka bankawa kwalejin wuta.
A riwayar TheCable, mutum tara yan ta'addan suka kashe.
Shugaban karamar hukumar Geidam, Hanarabul Ali Kolo, ya tabbatar da labarin inda yace yan ta'addan sun lalata dukiyoyin miliyoyi.
Kolo, duk da yana kasar Saudiyya don ibadar Umrah, yace wannan abin takaici ne amma har yanzu ba'a san adadin wadanda suka mutu ba.
Yace:
"Bisa labarin da na samu, Boko Haram sun kashe mutane kuma sun kona gidaje cikin har da kwalejin fasaha."
"Na tattaro cewa akwai yan biyu cikin wadanda harin ya shafa."
"Yanzu haka ina kokarin tuntubar hukumomin tsaro, amma babu hujjan cewa Sojoji sun kawar da su kamar yadda ake yadawa."
Harin Bam a gidan giya a Taraba: Kawo yanzu mutum 16 sun mutu
Adadin wadanda suka mutu a harin Bam din da aka kai gidan mashaya a Iware, karamar hukumar Ardo-Kola ya kai 16, masu idanuwan shaida sun bayyana.
Amma kakakin hukumar yan sandan jihar Taraba, DSP Abdulahi Usman, yace mutum shida kadai suka san sun mutu.
Punch ta ruwaito cewa mutane daban-daban wanda suka hada da James Audu, Mrs. Abaagu Esther da Musa David sun bayyana cewa mutum 10 da aka kai asibiti sun mutu kawo safiyar Laraba.
Asali: Legit.ng