Ramadaniyyat 1443: Tausaya wa Halittun Allah, Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Ramadaniyyat 1443: Tausaya wa Halittun Allah, Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo malami ne a tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar Bayero da Kano kuma shugaban cibiyar nazarin addinai a jami'ar.

A cikin jeringiyar janyo hankali na watar Ramadana da Malam ya yiwa lakabi da Ramadaniyyat, ya yi tsokaci kan tausayawa hallitun Allah.

Tausaya wa Halittun Allah

1. An karvo daga Abdullahi ɗan Amru (RA) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: Masu tausayi, (Allah) Mai Rahma zai tausaya musu, ku tausaya wa waɗanda suke bayan ƙasa, sai wanda yake sama (Allah) ya tausaya muku".

[Abu Dawud #4941 da Trimizi #1924, da Ahmad #6494].

2. A wannan hadisi Annabi (SAW) ya yi kira da a tausaya wa duk wata halitta da Allah ya yi, mutane ne ko dabbobi. Don haka ka zamanto mai tausaya wa kanka, mai tausaya wa wasu. Kada ka zama ɗan tsako samu ka ƙi dangi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun kai mummunan hari garin su gwamnan jiha, sun tafka ɓarna

3 Ka ji tausayin ƙarami da babba. Ka tausaya wa jahili da iliminka. Ka tausaya wa talaka da dukiyarka. Ka tausaya mai sabo da wa'azinka. Ka tausaya wa komai har dabbobi.

4. Duk wanda tausayinsa ga halittun Allah ya yawaita, to zai dace da tausayin Mahaliccinsa. Allah zai shigar da shi gidan karamci da ɗaukaka, sannan ya tsare shi daga azabar ƙabari, ya kuma sanya shi cikin inuwarsa ranar da babu inuwa sai tasa, domin kuwa duk waɗannan al'amura suna daga cikin Rahmar Allah.

Ramadaniyyat 1443: Tausaya wa Halittun Allah, Dr Sani Umar Rijiyar Lemo
Ramadaniyyat 1443: Tausaya wa Halittun Allah, Dr Sani Umar Rijiyar Lemo
Asali: Instagram

5. Dabi'ar tausayi a wajen bawa ita ce mafi girman hanyar samun rahmar Allah. Duk wani alheri na duniya da na lahira, Rahmar Allah sanadiyyarsa. Duk wanda ya rasa ɗabi'ar tausayi a zuciyarsa, to ya haramta wa kansa hanyar samun Rahmar Allah.

Kara karanta wannan

Babbar Matsala ta kunno kai a APC, Wani Babban jigo ya fice daga jam'iyyar, ya koma PDP

6. Bawa ba zai iya rayuwa ba sai tare da Rahmar Allah, ba zai iya wadatuwa ga barin ta ba daidai da ƙibtawar ido. Duk wata ni'ima da yake walwala a cikinta da kariya da yake samu daga duk wani abin ƙi, duka wannan bangare ne na Rahmar Allah.

7. Duk wanda yake son ya wanzar da ni'imar da yake ciki, ko ya samu ƙari a kan wadda yake da, to ya zamanto mai tausayi da jin ƙai ga al'umma. Allah ya sa mu dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng