Sata: Kotu Ta Ɗaure Tsohon Shugaban Wata Babbar Jami'ar Tarayya a Najeriya

Sata: Kotu Ta Ɗaure Tsohon Shugaban Wata Babbar Jami'ar Tarayya a Najeriya

  • Wata kotun majistare da ke Ile-Ife, Jihar Osun a ranar Alhamis ta daure tsohon shugaban daliban Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, Oyekan Ibukun a gidan gyaran hali
  • Hakan ya biyo bayan zarginsa da ake yi da yashe asusun kungiyar da ya shugabanta inda ya tura N720,0000 a watan Afirilun shekarar 2022, ga asusun bankinsa
  • An samu bayani akan cewa Oyekan tsohon shugaban kungiyar ne kuma dalibi ne a fannin likitanci a 2017, sai dai an tube shi bayan ya dauki nauyin kai wa dalibai hari

Osun - A ranar Alhamis, wata kotun majistare da ke Ile-Ife cikin Jihar Osun ta daure wani tsohon shugaban daliban Jami’ar Obafemi Awolowo a gidan gyaran hali bisa zarginsa da sace kudade daga asusun kungiyar wacce yanzu take da sabon shugaba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka basarake da wasu mutum 24, sun sace babura a Benue

The Punch ta tattaro bayanai kan yadda Onyekan ya rike kujerar shugaban kungiyar sannan kuma dalibi ne na fannin likitanci a shekarar 2017, kuma an tsige shi daga kujerar bisa zarginsa da daukar nauyin wata kungiya wurin kai farmaki ga dalibai.

Sata: Kotu Ta Ɗaure Tsohon Shugaban Wata Jami'ar Tarayya a Najeriya
Sata: Kotu Ta Ɗaure Tsohon Shugaban Jami'ar OAU. Hoto: Oyekan Ibukun.
Asali: Facebook

A shekarar 2022, an zarge shi da kwashe N720,000 daga asusun kungiyar inda ya tura wani asusu mai suna Bello Oyekunle Azeez a ranar 8 ga watan Afirilun 2022, kamar yadda The Eagle Online ta ruwaito.

A wata takarda wacce wani banki ya tura, a ranar 12 ga watan Afirilun 2022, mai taken, ‘Bukatar bincike akan asusu mai lamba: 1012121930 - Obafemi Awolowo University Union, wacce shugabanta, Olayiwola Festus ya ke jagoranta.

Banki ya tabbatar da fitar N720,000 ta yanar gizo daga tsohon shugaban kungiyar mai suna Ibukun Oyediran Oyekan zuwa asusun Oyekunle na wani bankin.

Kara karanta wannan

Idan dai cancanta ake bi’da shugabancin Najeriya sai Amaechi – Sarkin Dutse

Sakataren harkokin kudade na kungiyar ne ya fara samun bayani akan fitar kudin

A bangarensa, sakataren harkar kudaden kungiyar, Oluwasegun Abiola a wata takarda da ya saki a ranar Talata, ya ce:

“Yayin da na samu sakon fitar kudin, na yi kokarin sanar da Babban Sakataren kungiyar da Shugabanta akan cewa ko sun ga sakon, inda suka ce ba su gani ba.
“Bayan sanar da bayanai akan lamarin ne wasu masu fatan ganin bayan masu mukaman kungiyar da aka zaba suka fara kananun maganganu.
“A ranar Talata, 12 ga watan Afirilu, manajan bankin ya sanar da ni cewa wani Ibukun Oyekan (Dr. Ibk) ne ya fitar da kudin sannan ya bukaci in je bankin don samun rahoton bincikensu.”

A ranar Laraba, jami’an tsaron OAU suka kama Oyekan daga nan suka mika shi ga ofishin ‘yan sandan Moore don a ci gaba da bincike.

Ya kasa cika sharuddan belin, hakan yasa aka garkame shi

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da Janar din Sojan Bogi kan damfarar miliyoyi

Bayan nan ne a ranar Alhamis aka tura shi kotu gaban alkalin majistaren, A. A. Ayeni na kotun Majistare ta 3 a Ile-Ife inda aka zarge shi da hada makircin sata da kuma yin satar.

An kulle Oyekan wanda ya ki amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa a gidan gyaran halin Kosere da ke Ile-Ife bayan gaza cika sharuddan beli. Daga nan aka dage sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Afirilu.

Kakakin kungiyar daliban, Ogunperi Taofeek ya ce an bukaci kudin belin Dr. IBK N500,000, sai dai ya gaza biya, hakan yasa aka garkame shi a gidan yarin.

Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur

A wani labarin, Yan sanda a Jihar Katsina, a ranar Litinin sun yi holen wani Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, mazaunin Kasuwar Mata Street a Karamar Hukumar Funtua saboda damfarar wata tsohuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari na kashe N10bn a wata wajen ciyar da dalibai, FG

Ya wawushe mata dukkan kudinta na garatuti ta hanyar amfani da katin ta na banki wato ATM inda ya siya mota da babur da kudin, Vanguard ta ruwaito.

An taba kama mayaudarin, wanda ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar sauya musu katinsu na ATM a baya amma daga bisani ya fito daga gidan yari kuma ya cigaba da laifin, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164