Hamshakin mai arzikin duniya, Elon Musk ya taya Twitter kan $43bn, zai siye ta baki daya

Hamshakin mai arzikin duniya, Elon Musk ya taya Twitter kan $43bn, zai siye ta baki daya

  • Attajirin 'dan kasuwan da yafi kowa kudi a duniya ya bukaci kamfanin Twitter ta sayar masa da manhajar kafar sada zumuntar zamanin
  • Elon Musk yafi kowa narka hannun jari a kamfanin saboda ya yi imani da cewa wuri ne da ke bawa kowa damar bayyana ra'ayinsa, amma daga baya ya gane akasin haka
  • A cewarsa, kamfanin na bukatar zama na mutum daya, idan kuma kamfanin basu amince da farashin da ya taya ba, zai sake tunani a matsayinsa na mai kaso a kamfanin

Mutumin da ya fi kowa kudi a duniya, Elon Musk yana son siyan Twitter don ya maida shi mallakinsa, mujallar Bloomberg ta ruwaito.

Kamfanin Twitter ta sanar a ranar Alhamis cewa, Elon Musk, wanda yafi kowa hannun jari a Kamfanin, ya bukaci a siyar masa da sauran hannayen jarin manhajar kafar sada zumuntar zamanin a kan $54.20 ga duk hannun jari, wanda gaba daya darajarsa tafi $43 biliyan.

Kara karanta wannan

Bana 'yan crypto za su kudance: CEO a crypto ya yi hasashe, farashin bitcoin zai kai N41m

Hamshakin mai arzikin duniya, Elon Musk ya taya Twitter kan $43bn
Hamshakin mai arzikin duniya, Elon Musk ya taya Twitter kan $43bn. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, a cewar Musk, wannan farashin shine iya abunda zai iya siya, idan kuma basu amince da hakan ba, zai sake tunani a kan matsayinsa na mai hannun jari.

Ya ce "Na narka hannun jari a kamfanin Twitter saboda nayi imani da yadda cewa wuri ne wanda ke ba wa kowa damar bayyana ra'ayinsa a fadin duniya, sannan nayi imani da cewa bayyana ra'ayi shi ne mahimmin abunda da ke tabbatar da damakaradiyya."

Sai dai, tun lokacin da na narka hannun jari na gano cewa kamfanin ba zai iya taka mahimmiyar rawa wajen magance damuwar al'umma ba a halin da yake ciki yanzu. Akwai bukatar maida Twitter kamfanin mutum guda.

"Saboda haka, ina so in siya gaba daya kamfanin Twitter akan $54.20 ga duk hannun jari daya kudi a hannu, na fara narka hannun jari kashi 54 bisa dari a rana daya kafin in sake narka wani kashi 38 bisa dari a rana kafin a sanar da hakan ga kowa. Yadda na bukaci a siyar min shine iya yadda zan iya siya kuma ba zan kara ko kwandala ba, idan ba'a amince da hakan ba, zan sake tunani a kan matsayina na mai hannun jari a kamfanin."

Kara karanta wannan

Ko Buhari ya sauka matsalar tsaro ba za ta kare ba, Fadar Buhari ga dattawan Arewa

Twitter ta bayyana yadda tayin Musk, sannan za tayi tunani idan masu hannayen jari za su yi amanna da hakan ko kuma za ta cigaba da kasancewa Kamfanin mutane da dama.

Da farko Musk ya yi watsi da shirin shiga kwamitin masu kula da Twitter, ana gab da lokacinsa zai fara. Da ya amince da matsayin da hakan ya kange shi daga mallakar Kamfanin.

Sunayen biloniyoyi 87 na duniya: Dangote ya fi kowa kudi a Afrika, Elon Musk ya ninka shi sau 15

A wani labari na daban, mujallar Forbes ta saki jerin sunayen wadanda suka fi kowa dukiya a duniya, wanda takwas daga cikin goma na farko 'yan kasar Amurka ne, sai daya daga Faransa da kuma daya daga Indiya.

Har yanzu, Amurka ce ke mulkar duniya, wacce ke da biloniyoyi 735 da jimillar dukiyar $4.7 tiriliyan, duk da Elon Musk, wanda yazo na farko a jerin sunayen biloniyoyin duniya a karo na farko sama da Jeff Bezos.

Kara karanta wannan

Yaudara da neman goyon baya: Martanin Shehu Sani kan ikirarin Osinbajo na bin sahun Buhari

Independent UK ta ruwaito yadda Musk ke da $2 biliyan kacal a shekarar 2012, hakan na nufin ya tara sama da $218 biliyan (sama da N90.62 tiriliyan) cikin shekaru goma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng