Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da tsaffin shugabanni da masu ci, Buhari zai gana da Hafsoshin tsaro

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da tsaffin shugabanni da masu ci, Buhari zai gana da Hafsoshin tsaro

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai tattauna da shugabannin hukumomin tsaron ƙasar nan ranar Talata mai zuwa
  • A ranar Alhamis da muke ci, Shugaban ya gana da majalisar magabatan ƙasar nan da ta ƙunshi shuwagabannin Najeriya
  • Wannan matakan na zuwa ne a lokacin da matsalar tsaro ta ƙara tabarbarewa musamman a arewa

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya shirya taro da shugabannin hukumomin tsaron ƙasar nan baki ɗaya ranar Talata, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Wannan taron na su na zuwa ne dai-dai lokacin da matsalar tsaro ta yi wa Najeriya katutu a kusan kowane sashin kasa.

A yau Alhamis ne shugaban kasan ya jagoranci taron majalisar shuwagabanni ta ƙasa a fadar gwamnatin tarayya Aso Rock dake birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisar Shugabannin Ƙasa sun sanya ranar ƙidaya yawan Yan Najeriya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da tsaffin shugabanni da masu ci, Buhari zai gana da Hafsoshin tsaro Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna cewa tattaunawar ƙusoshin ƙasar ya maida hankali ne kan tattalin arziƙi da kuma matsalar tsaro da ta ƙi ci taƙi cinye wa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taron wanda aka fara da misalin ƙarfe 10:00 na safiya, ya samu halartan mataimakin shugaban ƙasa, Fafesa Yemi Osinbajo, Sakataren gwamnati, Boss Mustapha.

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Babagana Monguno, da kuma shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, duk sun halarci taron.

Tsofaffin shugabannin Najeriya da Gwamnoni sun halarci taron

Tsofaffin shugabannin Najeriya da suka halarci ɗakin taron su ne, Abdulsalami Abubakar, Goodluck Jonathan da Yakubu Gowon. Sauran kuma sun halarci taron ta fasahar zamani Virtually.

Gwamnonin da suka samu damar halartar wurin taron sun haɗa da, Hope Uzodinma na Imo, Kayode Fayemi na Ekiti, Nasiru El-Rufai na Kaduna da Bello Matawalle na Zamfara.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada umurnin garkame matasa biyu kan laifin 'ba haya' cikin Masallaci

Haka nan kuma sauran gwamnonin sun halarci taron ta hanyar amfani da fasahar zamani wato Virtually, kamar yadda The Cable ta rahoto.

A wani labarin na daban kuma Abinda shugaba Buhari ya faɗa wa Gwamnan APC bayan sanar da shi aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya sanar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takara a 2023.

Wata majiya ta bayyana cewa shugbaan ya ƙarfafa wa gwamnan guiwa ya cigaba da kokarin cika burinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262