Illoli da hadarin zama da mace guda daya, Sheikh Aminu Daurawa

Illoli da hadarin zama da mace guda daya, Sheikh Aminu Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

Illoli da hadarin zama da mace guda daya, Sheikh Aminu Daurawa

Zama da mace daya yana kawo illoli da dama ga magidanci da su mata kansu da kuma al`umma.

****

ILLOLI GA MAGIDANCI.

1:-Yana rage masa nishadin aure.

2:-Yana kawo tsufa da wuri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3:-Yana saka maigida cikin damuwa

4:-Yana saka wa mace ta rika daga masa kai, tayi masa yadda taso saboda ta san ba shi da yadda zai yi.

5:-Yana rage masa samun soyayya da tarairaya da kulawa da ya cancanta a matsayinsa na maigida.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: An Kama Wani Ba Amurke Da Bindigu a Filin Jiragen Sama Na Mohammed Murtala a Legas

6:-Yakan hana shi tantance so na gaskiya daga bangaren matarsa ko wanin haka.

****

ILLOLI GA SU MATAN.

1:-Yana hana wadansu samun mazajen aure.

2:-Yana dorawa matar gida aiyukan da suka shige misali kamar, kulawa da maigida, yaran gida da ita ma kanta.

3:-Yakan hana mace samun isasshen hutu da kuma lokacin kulawa da kanta.

4:-Yana rage wa mace kuzarin nuna soyayya ga maigidanta.

5:-Yana saka matar gida cikin tsoro da fargaba maras yankewa na ko za ai mata kishiya.

6:-Yana haifar da rashin amincewarta ga maigidanta da dauwamar da tuhuma ta har abada.

7:-Yana saka mace cikin shirin yaki da dawainiyar dakon makamai marasa ranar yankewa na nuna kin ayi mata kishiya.

8:-Yana saka mata yawan zargi ga dukkan matan da suke da alaka da maigidanta ko ma wace iri ce koda ma yar uwa ce ko abokiyar kasuwancinsa.

9:-Yana kara mata zafin kishi da rashin nutsuwa marasa ranar yankewa.

Kara karanta wannan

Dan baiwa: Bidiyon mai shekaru 8 da ya haddace Al-Qur'ani da wasu littatafai a Zaria

****

Sheikh Aminu Daurawa
Illoli da hadarin zama da mace guda daya, Sheikh Aminu Daurawa Hoto: Sunnah TV
Asali: UGC

ILLOLIN GA AL`UMMA

1:-Yana haifar da karuwar mata marasa aure.

2:-Yana bunkasa yawan zawarawa acikin al`umma.

3:-Yana dorawa al`umma karin nauyin kulawa da mata iyayen marayu da marayun kansu.

4:-Yana bunkasa zinace-zinace a cikin al`umma.

5:-Yana rage tausayi da son bada taimako da agaji daga zukatan al`umma.

6:-Yana kara saka fargaba da tsoro a zukatan iyaye wadanda suke da `ya`ya mata a gaba.

7:-Yana bunkasa kasuwar malaman tsibbu da bokaye.

WADAN NAN SU NE KADAN DAGA ILLOLIN ZAMA DA MACE DAYA,

DA FATAN MAGIDANTA ZASU GANE,

SU KUMA MATA ZA SU TAIMAKAWA JUNANSU WAJEN TUNAWA MAI GIDA YA QARA AURE

Asali: Legit.ng

Online view pixel