'Yan Bindigan Ba Su Yi Harbi Ko Sau Ɗaya Ba', Ganau Ya Magantu Kan Yadda Aka Sace Ɗaliban Zamfara

'Yan Bindigan Ba Su Yi Harbi Ko Sau Ɗaya Ba', Ganau Ya Magantu Kan Yadda Aka Sace Ɗaliban Zamfara

  • ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mata 5 cikin daliban kwalejin lafiya ta fasaha da ke garin Tsafe, hedkwatar karamar hukumar Tsafe da ke Zamfara
  • Kamar yadda mazauna yankin suka bayyana, ko harbi daya basu yi ba sai dai sun balle kofa ne inda suka afka dakin daliban suka sace su
  • An samu bayanai akan yadda ‘yan bindigan suka kwashe daliban da karfi da yaji kuma suka keta da su daji a kasa har sai da suka gaji da tafiya

Zamfara -’Yan bindigan da suka sace dalibai a kwalejin lafiya ta fasaha da ke Tsafe, hedkwatar karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara basu yi harbi ko daya ba a cewar wani mazaunin yankin.

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga suka yi dirar mikiya a cikin dakunan dalibai mata da ke wajen makarantar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka wani, suka sace 'yarsa mai shekaru 15 a Zaria

'Yan Bindigan Ba Su Yi Harbu Ko Sau Daya Ba', Ganau Ya Magantu Kan Yadda Aka Sace Ɗaliban Zamfara
'Ko Sau Daya Ba Su Yi Harbi Ba', Ganau Ya Magantu Kan Yadda Aka Sace Ɗaliban Zamfara. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mazauna yankin sun shaida yadda ‘yan bindiga suka kai hari dakunan dalibai da ke wajen makarantar.

Ita ma News Break ta rahaoto cewa dakunan suna wajen gari ne kuma dalibai sun dade suna zama a wurin na tsawon lokaci.

Sun saki daya daga cikinsu

Kamar yadda wani Adamu wanda mazaunin yankin ne ya shaida wa Daily Trust:

“Akwai rukunin dakuna biyu ne da dalibai suke zama na wajen makarantar kuma lokacin da mutanen suka isa basu yi harbi ko daya ba.
“Sun balle kofa ne inda suka afka dakunan dalibai suka saci 5. Wadanda ma suke gefen dakunan ba su san abinda ke faruwa ba sai da safe saboda ko harbi daya basu yi ba.
“Bayan sun dauke daliban sun ja su zuwa daji inda suka dinga tafiya a kasa har sai da daya daga cikinsu ta gaza tafiya. Daga nan ne suka sake ta, daya daga cikinsu ya daura ta a babur ya dawo da ita cikin gari sannan ya ce ta tafi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka basarake da wasu mutum 24, sun sace babura a Benue

“Yayin da suke tafiyar cikin dajin sun sanar da daliban cewa kudin fansa kadai suke bukata kuma ba za su ci zarafinsu ba.”

Ba a samu damar tattaunawa da Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin ba, SP Muhammadu Shehu, har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel