Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game da shugaban cibiyar Kididdigan Najeriya da ya mutu yau
A ranar Laraba, shugaban cibiyar bahasi, lissafi da kididdigan tarayyar Najeriya, Dakta Simon Harry, ya rigamu gidan gaskiya.
Hakan ya biyo bayan rashin lafiyar da yayi fama da shi bayan garzayawa da shi asibiti.
An samu jita-jitan mutuwarsa ranar Asabar, karshen makon da ya gabata amma diraktan yada labarai da hulda da jama'a cibiyar NBS, Sunday Ichedi, ya karyata rahotannin.
Amma da safiyar yau Laraba, ya tabbatar da cewa lallai yanzu ya mutu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga Abubuwa biyar da ya kamata ka sani game da marigayin:
1. Dan asalin jihar Flato ne, Arewa maso tsakiyar Najeriya
2. Shugaba Buhari ya nada shi shugaban mai kididdigan Najeriya a Agustan 2021
3. Ya shiga aiki cibiyar NBS a shekarar 1992 kuma ya cigaba da aiki har ya zama dirakta a 2019
4. Gabanin zama shugaban cibiyar, ya kasance diraktan shirye-shirye na cibiyar
5. Ya kwashe kimanin shekaru 30 yana aikin gwamnati
Gwamnatin Buhari: Ba Najeriya kadai ke fama da tsadar kayan abinci da man fetur ba
Gwamnatin tarayya ta ce karin da aka samu a farashin wasu kayan abinci, fetur, diesel da sauran kayayyaki abune da ake fama da shi a duniya gabaki daya, ba wai iya wata kasa bace.
Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, ya kara da cewar gabatar da lamarin a matsayin matsalar Najeriya makirci ne, rashin gaskiya da kuma batarwa.
Yace:
“Wannan kididdiga da ake amfani da shi makirci ne karara. Wadanda ke yayata wannan alkaluman ba tare da daura su a ma’auni ba rabin wayo ne da su.
“Mu duba farashin kayan abinci da fetur. Ku duba farashin kayan abinci a sauran kasashe, musamman UK da US ta Google, za ku ga cewa sun tashi.”
Asali: Legit.ng