Jirgin Abj-Kd: Ku saki kwamandoji da masu daukar nauyinmu 16 matsayin fansar wadanda muka sace, Yan bindiga
- Yan ta'addan da suka dasa Bam layin dogon Abuja-Kaduna sun bayyana bukatarsu ga gwamnatin tarayya
- A bukatarsu, suna son a saki wasu kwamandoji da masu daukar nauyinsu mutum goma sha shida (16)
- Majiyoyi sun bayyana cewa sun fara tattaunawa da wakilan gwamnatin tarayya
Yan bindigan da suka kai hari jirgin kasan Abuja, suna bukatar a saki kwamandojinsu 16 dake tsare hannun gwamnati don su saki wadanda suka sace a harin ranar 28 ga Maris.
Majiyoyi da dama sun bayyana cewa yan bindiga sun kai harin ne saboda mika wannan bukata.
A ranar Litinin, Punch ta ruwaito cewa yanzu haka ana tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da yan bindigan.
Wani babban jami'in gwamnati da aka sakaye sunansa yace yan bindigan sun wahala bisa kama kwamandoji da masu daukar nauyinsu.
Yace:
"Yan bindigan sun tuntubi gwamnati amma abin yanzu ta hada da hukumar Interpol saboda suna da masu daukar nauyinsu daga kasashen waje."
"Suna son a saki mutanensu daga daure. Sun bukaci a saki kwamandoji da masu daukan nauyinsu 16 matsayin fansar wadanda suka sace a jirgin kasa."
"Mun damke wasu daga cikin kwamandoji da masu daukar nauyinsu a Dubai da Najeriya. Su 16 na daure yanzu. Ina kyautata zaton ba za'a sakesu ba."
Wani jami'in leken asiri ya tabbatar da haka inda yace lallai wadannan kwamandoji da masu daukar nauyinsu na hada kai da Boko Haram wajen kai hare-hare Kaduna, Neja, Zamfara, Katsina da sauransu.
Yace:
"Abinda suke so shine a saki fursunoni da kudi. Idan suka ce basu son kudi karya ne; kudi suke so da musanyan fursunoni. Suna hada kai da Boko Haram."
Mutum daya kadai suka saki, amma sun saki bidiyo 2
A makon da ya gabata, yan bindigan sun saki Diraktan bankin noma, Alwan Hassan.
A bidiyon farko da suka saki ranar Laraba 6 ga Afrilu, sun bayyana cewa ba kudi suke bukata ba, gwamnati ta san abinda suke bukata.
Sun haska bidiyon ne tare da Shugaban bankin noma, Alwan Hassan, inda suka ce zasu sake shi albarkacin tsufarsa da watar Ramadan.
A ranar Lahadi kuma suka sake sakin wata bidiyon inda wasu daga cikin wadanda suka sace suka yi magana.
Asali: Legit.ng