ICPC ta fallasa Sanatocin Kebbi, Jigawa da Taraba da suka yi gaba da kudin talakawa

ICPC ta fallasa Sanatocin Kebbi, Jigawa da Taraba da suka yi gaba da kudin talakawa

  • ICPC ta bada bayanin yadda wasu Sanatoci suka yi amfani da ofishinsu, suka ci kudin al’umma
  • Hukumar ICPC mai binciken cin hanci da rashawa a Najeriya ta bayyana wannan a wani rahotonta
  • Sanata Muhammad Adamu Aleiro ya na cikin wadanda aka bankado a binciken da ICPC ta gudanar

Abuja - A wani dogon rahoto da Premium Times ta fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa wadannan Sanatocin sun fito ne daga Kebbi, Taraba da Jigawa.

ICPC ta ce ‘yan majalisar sun bada kwangilolin ayyukan mazabu ba tare da bin ka’ida ba ga wasu kamfanoninsu, a karshe sai suka yi sama da fadi da kudin aikin.

Wannan ya na cikin rahoton CEPTi da hukumar ICPC ta fitar a kan kwangilolin mazabu da ‘yan majalisa ke yi. Rahoton ya bankado aikin asshan da ake tafkawa.

Kara karanta wannan

Yadda za a gwabza wajen zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC

Jaridar ta ce ICPC ta binciki kwangilolin mazabu watau ZIP har 490 da aka ba ‘yan majalisa, aka gano irin barnar da ma’aikatun gwamnati da ‘yan majalisar ke yi.

Kowane daya daga cikin wannan kwangila ya ci akalla Naira miliyan. Daga 2000 zuwa yau, ayyukan ZIP sun ci wa gwamnatin tarayya kusan Naira tiriliyan biyu.

Binciken da aka gudanar bai fallasa sunayen Sanatocin da suka ci amanar ofishinsu, su ka bada kwangila ga kamfaninsu ko kamfanonin da iyalansu suka mallaka.

Sanatocin Najeriya
Wasu Sanatoci a zaman majalisa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Su wanene da wannan aika-aika?

Amma jaridar ta gano su wanene su ka yi wannan aika-aika, lura da mazabun da aka bada ayyukan.

Sanata Muhammad Adamu Aleiro

Ana zargin Sanata Muhammad Adamu Aleiro ya ba kamfanin Voltricity Nig. Ltd kwangilar shigo da na’urorin ban ruwa a mazabarsa, amma har yau ba a raba kayan ba.

Kara karanta wannan

Ashe makiyaya ne ba ‘Yan bindiga ba – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan bidiyon da ke yawo

Sanatan na Kebbi ta tsakiya ya bada kwangiloli ga kamfaonin ‘ya ‘yansa kamar Alliance Trading Ltd, Hummingbird Projects da Services Intll Ltd da Puranova Nig. Ltd.

Sanata Emmanuel Bwacha

Sai kuma Emmanuel Bwacha mai wakiltar Kudancin Taraba a majalisar dattawa, ya bada kwangilar gyara ajin karatun jami’ar tarayya da ke Wukari ga kamfaninsa.

A cewar ICPC, kamfaninsa na Eloheem Educational Management and Schools Ltd ya samu kwangila. Sannan ana zargin ya yi sama da fadi da kudin wasu ayyukan.

Sanata Sabo Mohammed

Na karshe a jerin shi ne Sanatan Kudu maso yammacin Jigawa da ya ba kamfanin ‘yanuwansa (Schramm Global Services Ltd) kwangilar shigo da wasu manyan motoci.

Daga bisani, motocin nan sun kare ne a hannun wani ‘danuwan Sanatan da shi aka ba kwangilar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng