Hukumar EFCC ta gurfanar da Janar din Sojan Bogi kan damfarar miliyoyi
- Bayan watanni biyu a tsare, Janar din sojan bogi da yace Shugaba Buhari Ya Zabeshi a Matsayin Shugaban Rundunar Sojin Kasa ya gurfana gaban kuliya
- Ya damfari wani kamfani da sunan zai yi amfani da kudin wajen neman shafa'a wajen Shugaba Buhari
- Ana zarginsa da aikata laifuka daban-daban akalla guda goma sha uku
Hukumar EFCC reshen jihar Legas ranar Litinin, 11 ga watan Afrilu, 2022 ta gurfanar da Bolarin Abiodun wani janar din sojin kasa na bogi a gaban mai shari’a Oluwatoyin Taiwo na kotu ta musamman dake Ikeja, Legas.
Bolarin ya gurfana ne kan tuhume-tuhume goma sha uku wanda suka hada da zamba, karya da samar da takardun bogi da yaudara ta kudi nera miliyan dari biyu da sittin da shida da dari biyar.
Hukumar ta bayyana hakan ne a jawabin da ta fitar ranar Litinin, 11 ga Afrilu, 2022.
Wanda ake tuhumar ya bayyana kansa a matsayin janar din sojin kasa, inda ya zambaci kamfanin Kodef Clearing Resources, cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabe shi a matsayin shugaban rundunar sojin kasa kuma yana bukatar wasu kudade don cimma burin nasa.
An kama shine a gidan sa dake Alagbado, jihar Legas ranar Laraba, 12 ga watan Janairu, 2022 inda aka kama shi da takardun bogi da suka hada da shaidar kama aiki a matsayin shugaban rundunar sojin kasa wacce shugaba Buhari ya sama hannu.
A takardar ya yi karyar cewa yana so ya biya wasu kudade a asusun gwamnatin tarayya a matsayin wasu sharuda da zai cika don samun aikin.
Mai shari’a ya daga ci gaba da sauraren karar zuwa Alhamis, April, 2022, inda ya umarci a ajiye wanda ake tuhuma a gidan gyara halinka na Ikoyi, jihar Legas.
Karfin Hali
A watan Junairu, Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta damke wani Janar din Soja na karya kan zargin damfarar N270m (Milyan dari biyu da saba'in).
Ya karbi kudin ne da sunan neman kamun kafa don shugaba Buhari ya nadashi babban hafsan Sojin tarayya.
Asali: Legit.ng