Shin da gaske Shugaba Buhari ya sake shillawa Landan ganin Likita?
- Fadar shugaban kasa ta karyata rahotannin dake cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shilla Landan
- Hadimin na musamman ga shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai yace Buhari na nan a Abuja
- Shugaba Buhari a kowace shekara ya kan tafi kasar Ingila duba likitocinsa tun da yace yana fama da ciwon kunne
Abuja - Rahotanni sun bazu a wasu kafafen yada labarai cewa an garzaya da Shugaba Muhammadu Buhari birnin Landan cikin gaggawa don sake ganin Likita.
Rahoton na Sahara Reporters ya nuna cewa shugaban kasan zai kwashe kwanaki ashirin a Ingila.
Rahoton ya nakalto mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, da cewa daga Landan ma garin Daura zai je bikin Sallah.
Amma hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, sun saki jawabin cewa babu gaskiya tattare da labarin tafiyar Buhari Landan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bashir Ahmad a jawabin da ya daura a shafinsa na Tuwita yace:
"Labarin dake yawo cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tafi hutun kwanaki 20 Landan karya ne."
"Shugaban kasa na Abuja kuma ba shi da niyyar zuwa Landan."
Dan Najeriya ya bude wurin abincin gargajiya a London, Turawa da bakar fata ke layin siya
A wani labarin kuwa, wani dan Najeriya mai suna Azeez ya fara aikin dafa shinkafar dafa-duka irin ta Najeriya a titin Landan, wanda yasa Turawa da dama suka yaba da irin dadin abincin.
A hoton da @IamOlajideAwe ya wallafa, anga wasu turawa na layin siyan abincin a gidan saida abinci.
Yayin hira a kafar sada zumunta da wakilin Legit.ng, Azeez ya bayyana yadda ya fara gudanar da siyar da abincin tare da wani, amma yanzu shi kadai ke gudanarwa.
Azeez ya ce:
"Ni dan Legas ne daga Surulere. Muna zama ne a Landan, saboda haka muka yanke shawarar kawo abincin cikin birnin. Mu biyu muka fara, amma yanzu da kaina nake yi."
Asali: Legit.ng