Kashi 70% na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai, UNICEF
- Asusun lamunin UNICEF ya bayyana cewa bincike ya nuna mafi akasarin yara a makarantun firamare kawai zuwa suke yi
- Bankin Duniya kuwa ya ce a nasa binciken kashi 70% na daliban makarantu ko jumla daya basu iya rubutawa
- Sun yi kira ga horar da Malaman makarantun da kuma sauya manhajar karatu
Kano - Asusun lamunin yara na majalisar dinkin duniya watau UNICEF ya ce kashi 70 cikin 100 na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai da ake koya musu a makaranta.
Masanin sadarwa na UNICEF, Mr Geoffrey Njoku, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a jihar Kano lokacin taron tattaunawa da manema labarai kan Sustainable Development Goals (SDGs).
A cewarsa, babban amfanin zuwa makaranta shine yaro ya iya karatu da lissafi na fari, rahoton kamfanin dillancin labarai NAN.
Yace:
"Tun 2010, mun yi kokarin magance matsalar yara milyan 10.5 da basu zuwa makaranta, amma duk da haka kashi 70% na yaran dake makarantar basu fahimtar darasi."
"Ya kamata mu hada adadin kashi 70% din nan kan milyan 10.5 da basu zuwa makaranta gaba daya don a maida hankali sosai kan lamarin."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Wajibi mu kawo sauyi bangaren ilimi ta hanyar horar da Malamai, canza manhajin karatu."
Yan shekaru 10 basu fahimtar jumla daya a Turanci
Hakazalika, Mr Rahama Farah, shugaban ofishin UNICEF dake Kano ya ce UNICEF da gwamnatin jihar Kano na hada kai wajen inganta ilmin Boko amma d sauran rina a kaba.
Farah, wanda ya samu wakilcin Elhadji Diop, ya ce:
"A cewar bankin duniya, Najeriya na fama da talaucin Ilimi saboda kashi 70% na yara yan shekara 10 basu iya hada jumla daya ko dan lissafi mai sauki."
"Saboda wajibi ne mu janyo hankalin masu ruwa da tsaki don magance matsalolin talauci a kasa.
Bugu da kari, Dr Chidi Ezinwa, Malami a tsangayar karatun jarida a jami'ar kimiya da fasaha dake Enugu yace cimma SDG's ba zai yiwu muddin ba'a cikka hakkin yara ba.
Asali: Legit.ng