Mun yi amfani da hoton Buhari don nunawa dalibai misalin gajiyayyen shugaba, Jami'ar da Pantami yayi karatu
- Jami'ar da Ministan Sadarwa yayi karatu ta bayyana dalilin da yasa tayi amfani da hoton Buhari wajen yiwa dalibai bayani a aji
- Jami'ar Robert Gordon dake Scotland tace Malamin yayi amfani da hoton ne wajen nuna misalin gajiyayyen shugaba
- Jami'ar RGU tace iyakan gwargwado tana baiwa Malamai yancin yin abinda suka ga dama don fahimtar dalibai
Wata jami'ar kasar Scotland, ta tabbatar da cewa lallai ta yi amfani da hoton Shugaba Muhammadu Buhari ne wajen nunawa dalibai misalin shugaban kasan da ya gaza.
Hoton ya nuna shugaban kasan bayan ya gama cin abinci a fadar Aso Villa.
Jami'ar da tayi wannan bayani, Robert Gordon University, ne Ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami, ya yi digirinsa na doktora.
A cewar Peoples Gazette, Jami'ar Robert Gordon University tace abinda Buhari ke yi na siffanta gajiyayyen shugaba a duniya, kuma tana baiwa Malamanta yancin iyakan gwargwado.
Jami'ar tace:
"Bidiyon na nuna Malami yana bayani ga dalibai kan misalan shugabanni daban-daban."
"Jami'ar RGU kuwa tana baiwa ma'aikatanta yanci."
Wannan jawabi ya biyo bayan bidiyon da ya bayyana kwanakin baya inda Malami a cikin aji yayi amfani da hoton Buhari matsayin shugaban da ya gaza.
Kalli bidiyon:
Asali: Legit.ng