Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

  • Rotimi Amaechi ya ce ya kamata yan Najeriya kullum su rika godewa shugaba Muhammadu Buhari
  • A cewar Amaechi, duk da kalamai maras dadi da ake yiwa shugaban kasa, bai daina ciyo bashi don gina titunan jirgi ba
  • Kawo yanzu, an kammala ginin layin dogon Abuja-Kaduna, Legas-Ibadan, da Warri-Itakpe

Ogun - Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a ranar Alhamis ya yi kira ga yan Najeriya su godewa Shugaba Muhammadu Buhari bisa ayyukan layin dogon jirgin kasan da take a fadin tarayya.

Amaechi ya bayyana hakan ne a Abeokuta, jihar Ogun yayin taron kaddamar da sabbin motocin hayan da gwamnatin jihar ta saya, rahoton Daily Trust.

Ya ce duk da sukar Buhari da ake yi kan karban basussukan kudi, bai yi kasa a gwiwa wajen gina layukan dogo ba tun da ya hau mulki a 2015, riwayar New Telegraph.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya zasu zabi APC a 2023 saboda gwamnati na ta yi namijin kokari, Shugaba Buhari

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya
Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya
Asali: Original

Yace:

"Abinda ya kamata yan Najeriya su yi shine gode mana. Na san ba zaku yi ba, wasu zasu yi, amma mafi akasari ba za suyi ba. Idan kai dan APC ne wajibi ne ka godewa shugaban kasa wajen duk da sukar karban bashin da ake masa bai daina gina layin dogo ba"
"Bashin da muke binku kenan, godiya. Saboda idan ka fadawa mutum yana kokari, zai kara dagewa."
"Kai yanzu ya bada izinin a sauya tsarin layin dogo zuwa Legas-Apapa-Epe-Lekki saboda kada a samu cinkoso a tashar ruwan Lekki kaman yadda ake fuskanta a Apapa kuma Satumba za'a kammala kuma a kaddamar."

Gwamnatin Buhari ta kashe Naira Biliyan 157 a aikin gina babbar gadar Neja-Delta

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ta ce kawo yanzu an batar da kudi har N157bn a aikin gadar nan ta Second Niger.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufa'i ya yi gaskiya, hanya ɗaya ce ta kawo karshen yan ta'adda, Tinubu ya magantu

Jaridar Daily Trust ta rahoto Ministar ta na wannan jawabi yayin da ta ziyarci wajen wannan aiki tare da shugabannin hukumar NSIA ta kasa a ranar Asabar.

Zainab Ahmed ta kai ziyara domin ganin yadda aikin yake tafiya ne tare da Farouk Gumel da Uche Orji wanda shi ne babban darektan NSIA da ke wannan aiki.

Hukumar Nigerian Sovereign Investment Authority ta ba kamfanin Julius Berger Nigeria Plc wannan katafaren aiki da ake sa ran za a gama a Agustan 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng