Inda ranka: Tashin hankali yayin da wani ya bude asusunsa ya ga takardu a madadin kudi

Inda ranka: Tashin hankali yayin da wani ya bude asusunsa ya ga takardu a madadin kudi

  • Wani dan Najeriya ya shiga tashin hankali da matukar mamaki bayan gano abin mamakin da ya faru da asusunsa
  • Ya bude ajiyarsa cikin asusun katako ya samu takarda a madadin kudin da ya jima yana tarawa, lamarin da ya bashi mamaki
  • Wani faifan bidiyo da ya dauka na lokacin bude asusun ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan Najeriya a intanet yayin da da dama ke yin tsokaci kan bacewar kudi a asusu

Farin cikin wani dan Najeriya ya koma nan take bayan da ya fasa asusunsa da zimman ganin kudi amma ya ga sabanin haka.

Mutumin da ke cikin rudani ya samu fararen takardu a madadin kudaden da yake adanawa mafi karancin daraja kamar N5, N10 da N20.

Wani mutum ya yi mamaki a bidiyo yayin da ya gano kudi a bankin alade ya koma takarda
Wani mutum ya yi mamaki a bidiyo yayin da kudin asusunsa suka koma takardu | Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

Cikin kaduwa da abin da ya samu a asusun ajiyarsa na katako, mutumin ya dauki bidiyon lamarin, wanda @instablog9ja ya yada a Instagram.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya bude wurin abincin gargajiya a London, Turawa da bakar fata ke layin siya

Abu mai ban mamaki shi ne na farko daga cikin lamurra da yawa da aka ruwaito na batar kudaden a asusu. Nasa ya dauki wani salo na daban duba da cewa kudinsa sun canja zuwa takardu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon ya jefa masu amfani da shafukan sada zumunta cikin rudani, kamar dai yadda wasu a intanet suka nuna shakku kan sahihancin batunsa, inda suka bayyana cewa watakila ba gaskiya bane.

Kalli bidion:

Martanin 'yan soshiyal midiya

@realestate_with_sandy:

"Dan uwa na ya zare kudina ya maye gurbinsu da takardu, ba komai bane zafi ooo."

@linqwa_:

"Idan da gaske ne.. Mutum zai sha wahala na shekaru 600...... wanda nake adanawa yanzu karka ka kuskura ka mayar dasu takardu idan ba kanaso ka taka da kafa har Abuja ba."

@yvonne_adaeze_onyeji:

"Ina tunani da babbar murya. Ina ga ya kamata duk ku hada asusunku da kanku maimakon ku saya daga hannun mutanen da kuke saya. Duniyar makirai."

Kara karanta wannan

Innalillahi wa’inna illahi raji’un: Allah ya yiwa sajan Funtua wanda harin jirgin kasa ya cika da shi rasuwa

@osahonplux:

"Abin da ke faruwa ke nan idan ka sayi asusun tsafi daga kasuwar kauyenku!"

@eberelauraobi_:

"Ku daina sayen asusu daga masu siyarwa maimakon haka ku je wurin kafinta cikin sauki ya kera muku."

Dan Najeriya ya bude wurin abincin gargajiya a London, Turawa da bakar fata ke layin siya

A wani labarin, wani dan Najeriya mai suna Azeez ya fara aikin dafa shinkafar dafa-duka irin ta Najeriya a titin Landan, wanda yasa Turawa da dama suka yaba da irin dadin abincin.

A hoton da @IamOlajideAwe ya wallafa, anga wasu turawa na layin siyan abincin a gidan saida abinci.

Yayin hira a kafar sada zumunta da wakilin Legit.ng, Azeez ya bayyana yadda ya fara gudanar da siyar da abincin tare da wani, amma yanzu shi kadai ke gudanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.