Kotu ta watsawa Abba Kyari kasa a ido, ta yi watsi da karar take hakkinsa da ya shigar

Kotu ta watsawa Abba Kyari kasa a ido, ta yi watsi da karar take hakkinsa da ya shigar

  • Hukumar NDLEA ta samu nasararta ta farko kan dan sandan da aka dakatar DCP Abba Kyari
  • Kotun da Abba Kyari ya shigar da kara kan NDLEA ta yi watsi da karar bayan lauyansa ya ki zuwa kotu
  • Abba Kyari ya shigar da kara kotu kan take masa hakki matsayin bil adama da NDLEA ta yi

Abuja - Babbar kotun tarayya dake Abuja, ranar Alhamis, ta yi watsi da karar take hakkin dan Adam da dakataccen DCP Abba Kyari ya shigar kan hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi NDLEA.

Alkali Inyang Ekwo ya yi watsi da karar ne bayan Lauyan NDLEA, Joseph Sunday, ya bukaci kotu tayi watsi da ita, rahoton kamfanin dillancin labarai NAN.

Kotu 15
Kotu ta watsawa Abba Kyari kasa a ido, ta yi watsi da karar take hakkinsa da ya shigar
Asali: Twitter

An nemi Cynthia Ikena, lauyan Abba Kyari an rasa yayinda lokacin zaman kotu yayi.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: PDP Ta Sha Kaye a Kotu, An Ƙi Ƙwace Kujerar Gwamna Ayade Da Ya Koma Jam'iyyar APC

Alkali Ekwo yace an sanar da shi cewa Lauyan Abba Kyari ba zai samu damar zuwa ba kuma ya bukaci a dage zaman.

Amma lauyan NDLEA yace wasikar da lauyan Abba Kyari ya bayar ya sabawa dokokin kotu. Ya bukaci kotu tayi watsi da wasikar.

Alkalin kotun kuwa bayan dubi cikin lamarin yayi watsi da karar.

Kotu ta sa ranar da za a saurari shari’ar damka Abba Kyari ga hukumomin kasar Amurka

A bangare guda, babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja, ya daga wata kara da ake yi da babban jami’in ‘dan sandan nan da aka dakatar, DCP Abba Kyari.

Vanguard ta fitar da rahoto cewa a ranar Litinin aka zauna kan karar da aka shigar domin hana gwamnatin tarayya mika Abba Kyari ga hukumomin Amurka.

Kara karanta wannan

Sojoji sun dakile mota dauke da N100m kudin fansa za'a kaiwa yan bindiga

Alkali ya daga wannan shari’a zuwa ranar 4 ga watan Yuli 2022 domin a cigaba da zama a kotu.

Wadanda aka shigar a wannan shari’a mai lamba ta FHC/ABJ/CS/854/2021 sun hada da rundunar ‘yan sandan Najeriya da Ministan shari’a, Abubakar Malami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng