Babban Kwamandan Boko Haram, Mustapha Ibn Kathir, ya mika wuya: DHQ
- Kwamandan rundunar yan ta'addan Boko Haram na Garin Ba-Abba, Saleh Mustapha, ya mika wuya
- Hedwatar Sojin tarayya ta bayyana irin nasarorin da dakarun Sojin kasa da sama suka samu cikin makonni biyu da suka gabata
- Kakakin hedkwatar yace kawo ranar 5 ga Afrilu, yan ta'adda 51,114; maza, mata da yara ne suka mika wuya.
Abuja - Hedkwatar Sojin Najeriya DHQ ta bayyana cewa babban kwamandan Boko Haram, Saleh Mustapha, ya mika wuya ga dakarun Sojin Operation Hadin Kai, a Arewa maso gabashin Najeriya.
Kawo yanzu jimillan yan Boko Haram 51,114 ne suka mika wuya, rahoton NAN.
Diraktan yada labarai na DHQ, Manjo Janar Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.
Manjo Janar Onyueko ya ce mika wuyar Mustapha wanda aka fi sani da Ibn Kathir wanda shine Kwamandan Garin Ba-Abba, babban nasara ne.
Yace kawo ranar 5 ga Afrilu, yan ta'adda 51,114; maza, mata da yara ne suka mika wuya.
Daga cikinsu akwai Maza 11,398, sannan mata da yara 24,335.
Ya ce a makonni biyu da suka gabata, Sojojin sun samu nasarar kwace Igwa daya, bindigogin Atilary biyu, GTS biyu da bindigogin baro jirage 3.
Ya kara da cewa:
"Hakazalika mun kwato harsasan NATO 7.62mm guda 600, bindigan gargajiya daya, harsasai 7.62mm guda 270, mota Toyota Buffalo, Golf Saloon, babura hudu, carbin harsasai shida, rigar Soji biyu, tutoci biyu, Keke Napep daya, da jirgin leken asiri daya."
Janar Onyeuko ya kara da cewa an kashe dimbin yan ta'adda kuma an damke infoma 22, yan Boko Haram 11, masu kai musu kaya uku, kuma an ceto fararen hula 30.
Bayan Watanni 10, Har Yanzu Ɗaliban Yauri Mata 11 Suna Hannun Ƴan Ta'adda
Sakamakon farmakin da fitaccen dan bindiga, Dogo Gide da yaransa suka kai Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi, sun sace dalibai da malamai sannan sun saki wasu, yanzu haka 11 daga cikin dalibai mata zasu cika watanni 10 a hannunsu.
A ranar 17 ga watan Yunin shekarar da ta gabata suka kai farmakin FGGC Birnin Yauri inda suka yi garkuwa da dalibai da yawa da malamai biyar.
Asali: Legit.ng