Matakai masu sauki da zaka bi wajen hada layin wayarka da NIN yayinda gwamnati ta toshe layukan 72m

Matakai masu sauki da zaka bi wajen hada layin wayarka da NIN yayinda gwamnati ta toshe layukan 72m

Bayan wata da watanni tana dage wa'adin rufe layukan wadanda basu hada lambar katin zaman dan kasa NIN da layukan waya ba, gwamnatin tarayya a ranar Litinin, 14 ga Afrilu, ta umurci kamfanin sadarwa su hana kira fita daga duk wani layin da ba'a hada ba.

Sakamakon wannan umurni, an toshe layuka milyan 72.77 daga kiran waya sai sun hada layukansu.

Legit ta tattaro muku yadda zaku iya hada layukan wayarku da NIN ga masu amfani da MTN, Glo, Airtel, and 9mobile.

Yadda zaka duba lambar NIN dinka

Idan ka je rijistar katin zama dan kasa a cibiyoyin da gwamnati ta ayyana, za'a baka wani takarda dauke da lambar NIN.

Idan ka yarda takardar kuma, zaka iya duba lambarka ta NIN a kan wayar ka.

Hukumar yin katin zama dan kasa NIMC, ta bukaci yan Najeriya su danna *346# a wayoyinsu don fito da lambar NIN.

Kara karanta wannan

Gonar kudi: Yadda matashi ya sayar da hoton tsaleliyar budurwa N600k a duniyar crypto

Masu amfani da MTN, Airtel, 9Mobile da Glo zasu iya amfani da lambar.

NCC da SIM
Matakai masu sauki da zaka bi wajen hada layin wayarka da NIN yayinda gwamnati ta toshe layukan 72m Hoto: NCC
Asali: UGC

Yadda zaka hada NIN da layin MTN

Ta hanyar yanar gizo

  • Shiga shafin yanar gizon MTN https://mtnonline.com/nin/
  • Zaka ga inda zaka rubuta sunanka
  • Sai ka sanya lambar wayarka ta MTN
  • Zaka sanya NIN dinka
  • Zaka sanya akwatin sakon email dinka
  • Sai ka dannan 'SUBMIT'

Idan ba ka son hadawa ta yanar gizo

  • Danna *785#
  • Sanya lambarka ta NIN, sai ka tura
  • Za'a sanar da kai ko yayi ko bai yi ba

Yadda zaka hada NIN da layin GLO ta akwatin sako (SMS)

  • Rubuta - UpdateNIN (bada tazara) lambarNIN (bada tazara) Sunanka na farko (bada tazara) sunanka na karshe
  • Sai ka tura 109

Yadda zaka hada NIN da layin Airtel

Kara karanta wannan

Shin ka hada layin wayarka da NIN amma har yanzu ba ka iya kira? Ga abinda zaka yi

  • Danna *121*1#
  • Rubuta lambar NIN dinka (lambobi 11)
  • Zaka samu sakon SMS

Yadda zaka hada NIN da layin 9mobile

  • Shiga shafin yanar gizo https://9mobile.com.ng/nin
  • Dannan waje mai kalar kore inda aka ce 'verify and link your NIN now'
  • Sanya lambar wayar da sauran bayanai

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng