An damke Lami Mairigima, matar da akayiwa lakabi da sarauniyar yan kwaya

An damke Lami Mairigima, matar da akayiwa lakabi da sarauniyar yan kwaya

  • Hukumar NDLEA ta cika hannu da sarauniyar yan kwaya a jihar Taraba, Lami Mai Rigima
  • Hukumar hana fasa kwabri ta damke Mai Rigima ne bayan kimanin shekara guda ana nemanta
  • Lami ce dilar kwayoyi dake baiwa kananan masu safarar kwaya a jihar Taraba

Jalingo - Hukumar hana safarar muggan kwayoyi NDLEA, ta sanar da damke sarauniyar yan kwaya, Lami Mairigima, wanda ke kaiwa masu fataucin mutane kwayoyi a jihar Taraba.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, a jawabin da ya fitar a Abuja ranar Laraba yace ta damketa ne bayan watanni da fara nemanta ruwa a jallo.

Babafemi yace sun fara farautarta ne a 2021 lokacin da masu safarar kwayoyi da dama suka ce ita ce dilarsu.

A ranar Litinin, 4 ga Afrilu aka gano Lami a garin Iware, karamar hukumar Ardo Kola ta jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Lami Mairigima
An damke Lami Mairigima, matar da akayiwa lakabi da sarauniyar yan kwaya Hoto: NDLEA
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, Babfemi yace jami'an hukumar NDLEA sun damke wani mai safarar kwayoyi, Emeka Okiru, da kwayoyin Tramol 32,700.

Yace an damkeshi ne a karamar hukumar Mubi, ranar Talata, 5 ga Afrilu, yayinda yake kokarin kasuwancin da abokan hajarsa da suka zo daga Kamaru.

Ya boye kwayoyin ne cikin buroshin fenti.

Jami'an 'yan sanda sun ki karbar cin hancin N500k bayan kama mota dankare da miyagun kwayoyi

A wani labarin kuwa, jami’an rundunar ta jihar Legas ta tabbatar da cewa ‘yan sandan Najeriya sun kama wata motar bas dauke da miyagun kwayoyi a unguwar Mile 2 da ke jihar Legas.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi a Legas.

Ya ce jami’an rundunar RRS sun damke wata mota kirar bas kuma sun kama wani Ojukwu Omanogho mai shekaru 36 , Hope Jumbo mai shekaru 40 da Oluwole Omojuyitan mai shekaru 40.

Kara karanta wannan

Jami'an 'yan sanda sun ki karbar cin hancin N500k bayan kama mota dankare da miyagun kwayoyi

Hundeyin ya ce a karon farko bincike ya nuna cewa kwayoyin na wani Alhaji ne wanda aka fi sani da Janar a Mushin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng