Garaɓasa: Gwamna ya rage wa ma'aikatan jiharsa lokacin aiki albarkacin Watan Ramadana

Garaɓasa: Gwamna ya rage wa ma'aikatan jiharsa lokacin aiki albarkacin Watan Ramadana

  • Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin gwamna Atiku Bagudu, ta rage wa ma'aikatan jihar yawan awannin aiki
  • A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ranar Laraba, tace ta rage awa ɗaya ɗaga cikin lokacin da ma'aikata ke shafewa a wurin aiki saboda Azumi
  • A cewarta, rangwamen da gwamna ya yi wa ma'aikata bai saɓa wa al'adar jihar Kebbi ba

Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi karƙashin jagorancin gwamna Atiku Bagudu, ta rage lokacin aiki ga ma'aikatan jihar Albarkacin Azumin watan Ramadana.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin ta rage awa ɗaya a kowace ranar aiki domin girmama watan Azumi da kuma sauƙaƙa wa ma'aikata.

Gwamnan jihar Kebb, Atiku Bagudu.
Garaɓasa: Gwamna ya rage wa ma'aikatan jiharsa lokacin aiki albarkacin Watan Ramadana Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da muƙaddashin shugaban ma'aikata na jihar Ƙebbi, Alhaji Safiyanu Garba-Bena, ya fitar ranar Laraba a Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Matar Aure mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure

Wane rangwame gwamnatin Kebbi ta yi wa ma'aikata?

Ya ce daga yanzun, ana tsammanin ma'aikata za su fara aiki daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa ƙarfe 3:00 na rana daga ranar Litinin zuwa ranar Alhamis na kowane mako.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kuma ya kara da cewa a ranar Jumu'a, lokacin aiki zai fara daga ƙarfe 8:00 na safiya zuwa karfe 12:00 na tsakar rana.

The Nation ta rahoto Wani sashin sanarwan da gwamnatin ta fitar ya ce:

"Wannan rangwame da gwamna Atiku Bagudu ya yi wa ma'aikata bai saɓa wa al'adar da aka kafa jihar Kebbi a kai ba."
"Kuma an yi duba da cewa rage awannin aikin zai taimaka wa ma'aikata wajen samun saukin ibadar watan Azumin Ramadana mai albarka da suka fara."

Legit.ng Hausa ta zanta da wani ma'aikacin gwamnati ɗan asalin jihar Kebbi, Jabir Musa Dododo, kuma ya shaida wa wakilin mu cewa gwamna ya yi abin da ya dace.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari a ayyana shiga tseren kujerar gwamna a zaɓen 2023, ya yi alƙawarin ba zai ci amana ba

Sani ya ce:

"Eh gwamna ya ɗauki matakin da ya dace domin tausayawa ma'aika a wannan watan mai alfarma (Ramadan) duba da yanayin zafi da ake ciki."

Mista Sani, wanda ɗan siyasa ne, ya faɗa wa wakilin mu cewa ma'aikatan Kebbi sun ji daɗin wannan rage lokaci kuma sun yaba wa gwamnati.

A wani labarin kuma ministan Shari'a Abubakar Malami ya faɗi gaskiya kan rahoton shiga takara a zaɓen 2023

Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya musanta rahoton cewa ya shiga tseren kujerar gwamnan Kebbi.

A wata sanarwa da kakakin ministan, Dakta Umar Jibrilu Gwandu, ya fitar yace wasu ne da suka ƙosa suke yayata jita-jitar amma ba gaskiya bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262