Tsohon shugaban EFCC Magu zai bar aiki, ya gagara samun karin matsayi zuwa AIG
- Lokacin yin ritayar tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Mista Ibrahim Magu ya gabato
- A farkon watan Mayun 2022 ne Ibrahim Magu zai cika shekara 60 a Duniya, ya yi shekara 32 a NPF
- Wannan zai sa babban jami'in tsaron ya yi ritaya daga aikin ‘dan sanda bai taba rike matsayin AIG ba
Abuja - Tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC na kasa, Ibrahim Magu ya na shirin yin ritaya gaba daya daga aikin ‘dan sanda a Najeriya.
The Cable ta fitar da fitar da wani rahoto na musamman a ranar Talata da ya nuna Ibrahim Magu zai bar aikinsa bayan ya gagara samun karin girma.
Zaman Magu Mataimakin Sufeta Janar watau AIG a gidan ‘yan sanda ya na neman ya gagara, yayin da lokacin yin ritaya kuma ya dumfaro jami’in.
A ranar 5 ga watan Mayun 2022 ne Ibrahim Magu zai ajiye aiki, ya shafe shekaru 31 a gidan ‘yan sanda. Wannan shi ne abin da dokar aikin NPF ta ce.
Sashe na 18 (8) na sabuwar dokar aikin ‘dan sanda ya tsaida lokacin ritayar ma’aikata. A ranar 5 ga watan Mayun 1962 ne aka haifi Mista Ibrahim Magu.
Babu maganar zama AIG
Hakan na nufin nan da wata guda tsohon shugaban na EFCC zai cika shekara 60. Rahoton ya ce har ya tafi hutun da ake zuwa kafin a kai ga ajiye aiki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Idan aka tafi a haka, jami’in tsaron da ya zama malamin bincike ba zai dandana matsayin AIG ba har abada, duk da cewa sa’aninsa sun kai wannan matsayi.
Hukumar PSC mai kula da aikin ‘yan sanda a Najeriya ta amince a karawa Magu matsayi zuwa Mataimakin Sufeta na kasa, amma dai hakan bai yiwu ba.
Zunuban Ibrahim Magu
Ana zargin Ibrahim Magu da aikata wasu laifuffuka da suka saba doka a lokacin da yake rike da EFCC, kusan wannan ya hana karin matsayinsa ya tabbata.
Kwamitin Ayo Salami da ya yi bincike ya bada shawarar a tsige Magu saboda ya gagara yin bayanin inda aka kai wasu kudi har N431,000,000.00 a EFCC.
Sannan ana tuhumar shi da batar da hujjoji da kuma yin rufa-rufa a binciken manya. Magu da lauyoyinsa sun musanya sakamakon binciken kwamitin.
An tono 'yan cuwa-cuwa
Dazu aka fahimci cewa binciken OHCSFNGR ya nuna cewa masu takardun samun aiki na karya a Gwamnati sun cika ma’aikatu da hukumomin kasar nan.
Folashade Yemi-Easan ta ce a shekarar 2021 aka gano cewa a wata ma’aikatar tarayyana da fiye da mutum 1000 masu amfani da takardun samun aikin bogi.
Asali: Legit.ng