Gabansa ba ya aiki: Tsohuwa mai shekaru 54 ta nemi saki a gaban kotu
- Wata mata mai shekaru 54 ta tafi gaban alkali, ta nemi a tsinka igiyar aurenta saboda rashin iya tabuka komai
- Ta koka kan yadda zamansu ya kasance tsawon shekaru, inda tace sam ba ya kula da ita ko danginta
- Ta koka kan yadda gabansa ba ya aiki, inda tace ta kai shi asibiti amma ya ki amfani da maganin da aka rubuta masa
Wata mata ‘yar shekara 54 mai suna Blessing Mormah ta garzaya wata kotun al’adu ta Igando inda ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda ganin cewa mijin ba a iya gamsar da ita wajen jima’i.
Matar mai sana'ar kwalliya mai suna Mormah ta roki kotu a ranar Talata da ta raba aurenta da ya shafe shekara 25 tana mai ikrarin cewa, dama an tilasta mata yin auren ne, The Nation ta ruwaito.
Hakazalika, ta bayyana yadda take dama dashi duk lokacin da rikici ya barke a tsakaninsu, inda tace korarta yake daga gidansa.
Batutuwan da ta shaidawa kotu
Ta ce ta gaji, kuma ba za ta iya ci gaba da zaman auren ba, inda ta kara da cewa:
“Har ila yau, gabansa ba ya aiki.
“Da na gano na kai shi asibiti aka rubuta masa magunguna amma bai taba amfani da su ba.
“Kullum cewa yake babu abin da ke damunsa.
"Shikenan, idan babu abin da yake damunka, to, ka sauke hakkinka, amma ba zai iya ba.
“Har ila yau, ba ya girmama dangina."
Ta kuma shaida wa kotu cewa ta nema mata saki saboda ta rabu da rakai, kana ta koka kan rashin lokacinta da bai dashi.
Ta kuma shaida wa kotun cewa sun shafe shekara guda basa tare don haka ta roki kotu ta ba damar ike yaransu, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Wanda ake kara, Mista David Mormah, bai samu damar halartar kotun ba balle ya bayar da nasa jawabin.
Daga baya shugaban kotun Mista Koledoye Adeniyi ya dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Mayu domin yanke hukunci.
Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan yari
A wani labarin, kotu ta yanke hukunci kan karar da aka shigar kan Shahararren matashin da ke ikirarin bai yarda da Allah ba, dan asalin jihar Kano, Mubarak Bala, ranar Talata, 5 ga Afrilu, 2022.
Wata babban kotun jihar Kano dake zamanta a Audu Bako Secretariat ta yanke masa hukuncin daurin shekaru ashirin da hudu a gidan gyaran hali bayan amsa laifukan da ake tuhumarsa da su.
Gabanin yanke masa hukunci, Mubarak ya bukaci kotu ta sassauta masa saboda bai aikata abubuwan da ake zarginsa da su ba don tada tarzoma.
Asali: Legit.ng