Da Dumi-Dumi: Rahoton na ayyana shiga takarar gwamnan Kebbi Ƙaryane, Malami
- Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya musanta rahoton cewa ya shiga tseren kujerar gwamnan Kebbi
- A wata sanarwa da kakakin ministan, Dakta Umar Jibrilu Gwandu, ya fitar yace wasu ne da suka ƙosa suke yayata jita-jitar amma ba gaskiya bane
- A cewarsa, idan lokaci ya yi Malami da kansa zai sanar a hukumance kuma labari zai karaɗe kowane shafin zumunta
Abuja - Antoni Janar na ƙasar nan kuma ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN) ya musanta rahoton dake cewa ya bayyana sha'awar neman kujerar gwamnan Kebbi, kamar yadda Dailytrust ta rahoto
Jita-jita ta fara yawo a kafafen sada zumunta cewa Ministan ya nuna sha'awar gaje kujerar gwamnan Kebbi mai ci, Atiku Bagudu, kuma da safiyar Talata rahoton ya ƙara yawaita.
A wata sanarwa da babban mai taimaka wa Ministan kan harkokin midiya da yaɗa labarai, Dakta Umar Jibrilu Gwandu, ya fitar a madadin Malami ya musanta rahoton.
Sanarwan mai taken, "Har yanzun ban bayyana shiga takara ba - Malami," ta ce karin haske kan lamarin ya zama wajibi duba da wasu kafafe sun fara yaɗa jita-jitar.
Punch ta rahoto wani sashin sanarwan ya ce:
"Gwandu ya ce lamarin ayyana shiga tseren wata kujerar siyasa ba harka ce da za'a yi ta a duƙunkune ba ko wani bangaren kafafen watsa labarai ne kaɗai za su rahoto."
"Rahoton ya samo asali ne daga son asani da kuma ƙosawar masoya da masu goyon baya da suka ƙagara."
"Gwandu ya ce idan lokacin da ya dace ya yi, za su ji daga bakin mai gayya mai aiki da kansa da kuma dukkam kafafe, masu ruwa da tsaki, masoya, mambobin jam'iyya da tawagar magoya baya."
Shin Malami ya nuna sha'awar zama gwamnan Kebbi?
Malami, wanda ɗan asalin jigar Kebbi ne, ya shafe wa'adi biyu a matsayin mamban gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kuma babban jigon jam'iyyar APC.
Rahoto ya nuna cewa a shekarar 2014, Malami ya sayi Fam ɗin sha'awar tsayawa takara a APC, amma ya sha kaye a hannun Atiku Bagudu a zaɓen fidda gwani.
A wani labarin kuma Tsohon shugaban jam'iyyar APC ta kasa ya ayyana shiga tseren takara a zaɓen 2023
A wurin bikin karin shekara, tsohon shugaban APC na ƙasa ya ayyana shiga takarar kujerar Sanata a zaɓe mai zuwa.
Kwamaret Adams Oshiomhole, ya ce lokaci ya yi da zai amsa kiran da mutane ke masa na ya wakilce su a majalisar dattawa.
Asali: Legit.ng