Jerin jihohin Najeriya 24 da basu samu masu zuba hannu jari daga kasashe waje ko daya ba
- Hukumar lissafin Najeriya ta saki rahoton zuba hannun jari daga kasashen waje da aka samu a shekarar 2021
- A cewar rahoton, Najeriya bata taba samun karancin masu zuba hannun jari irin wannan ba cikin shekaru 11
- Zuba hannun jarin attajirai daga kasashen waje ne daya daga cikin hanyoyi uku da kudi ke shigowa Najeriya
Hukumar lissafin tarayya NBS ta wallafa rahoton zuba hannun jari daga kasashen waje da jihohin Najeriya suka samu a shekarar 2021.
Legit.ng ta tattaro cewa a rahoton da aka saki, Najeriya ta samu kudi $698.7m na hannun jarin da yan kasashen waje suka zuba.
Zuba hannun jarin daga kasashen waje ne daya daga cikin hanyoyi uku da kudi ke shigowa Najeriya
A cewar rahoton da lissafi na NBS, kudin da aka samu a 2021 ne mafi karancin da Najeriya ta samu cikin shekaru 11.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga jerin jihohi 24 da basu samu masu zuba hannun jari ko guda ba a 2021:
1. Adamawa
2. Bauchi
3. Bayelsa
4. Benue
5. Borno
6. Cross River
7. Ebonyi
8. Edo
9. Enugu
10. Gombe
11. Imo
12. Jigawa
13. Kaduna
14. Katsina
15. Kebbi
16. Kogi
17. Nasarawa
18. Niger
19. Ondo
20. Plateau
21. Sokoto
22. Taraba
23. Yobe
24. Zamfara
An kashe N1.3trn amma wutar lantarki bata gyaru ba, ministar kudi
A wani labarin kuwa, ministar kasafin kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce kudade Naira tiriliyan 1.3 da gwamnatin tarayya ta tanadar a bangaren samar da wutar lantarki basu haifar da da mai ido ba, inji rahoton TheCable.
A ranar 1 ga Maris, 2017, FG ta amince da kashe N701bn domin inganta wutar lantarki ga Kamfanin Dillalan Wutar Lantarki ta Najeriya (NBET) domin biyan kudin da GenCos ke samarwa ga ma’aikatar wuta ta kasa na tsawon shekaru biyu.
An bayar kudaden ne domin tunkarar kalubalen kudi na wata-wata da GenCos ke fuskanta, yayin da kamfanonin rarraba wuta (DisCos) ke ci gaba da gazawa wajen biyan kudaden wutar lantarkin da ake rarrabawa duk wata.
Asali: Legit.ng