Mata mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure

Mata mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure

  • Wata mata saboda tsabar kishi ta ɗaɓa wa Maigidanta wuƙa har lahira saboda ya shaida mata zai ƙara Aure daga kauyen su
  • Lamarin ya auku a jihar Oyo, kuma rahoto ya nuna cewa Matar yar shekara 43 ta halaka Mijin ne yana tsaka da bacci
  • Bayan aikata wannan ɗanyen aikin, bayanai sun nuna cewa matar ta kai kanta Ofishin yan sanda

Oyo - Wata matar aure mai ɗauke da juna biyu, Omowunmi Joseph, yar shekara 43 dake zaune a yankin Odoye, Alaadorin, ƙaramar hukumar Ibadan ta arewa a jihar Oyo, ta daɓa wa mijinta wuka har lahira.

Daily trust ta rahoto cewa matar ta halaka Maigidanta, Joseph Nwankwo, yana tsaka da bacci da misalin ƙarfe 2:00 na daren ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Abun Kunya: Babban abokin Ango ya sace danƙareriyar kyautar Amarya mai tsada a Kano

Rahoto ya nuna cewa saɓani ya shiga tsakanin ma'auratan ne mako biyu da suka shuɗe lokacin da Mijin ya faɗa wa matarsa cewa zai ƙara Aure a karo na biyu a can mahaifarsa.

Wata mata ta halaka mijinta.
Mata mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar wata majiya da muka samu, bayan kashe mijinta, Omowunmi ta kai kanta Ofishin yan sanda na Iyaganku, amma kuma jami'ai suka maida ta Caji Ofis ɗin Yemetu, mafi kusa da inda lamarin ya faru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk wani kokarin jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Oyo, Adewale Osifeso, kan abun da ya faru ya ci tura.

Ɗan sanda ya mutu a Hotel

Wani ɗan sanda na sashin Operations a Ofishin Eleyele dake Ibadan, Michael Ogunlade, ya rasa rayuwarsa yana tsaka da saduwa da masoyiyarsa a Otal.

Wata majiya a Otal ɗin ta shaida wa wakilin jaridar cewa ya haɗu da masoyan biyu a matattakalan hawa Bene yayin da suke kan hanyar zuwa ɗaki.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban jam'iyyar APC ta kasa ya ayyana shiga tseren takara a zaɓen 2023

Ya ce mintuna kaɗan bayan haka, matar ta sakko da gudu tana kuka ta faɗa musu cewa mutumin da suke tare ya mutu.

"Nan take muka sanar da yan sanda kuma suka yi gaggawar zuwa wurin, kafin su kai shi Asibiti rai ya yi halinsa," inji majiyar.

A wani labarin kuma Uwar gida ta danna wa Mijinta wuka har lahira daga zuwa bankwana zai koma dakin Amarya

Tsagwaron kishin mata ya yi sanadin rasuwar wani Mai mata biyu yayin da yake yi wa Uwar gida bankwana zai koma dakin Amarya.

Rahoto ya nuna cewa Uwar gidan mai suna Atika ta daba wa mijinsu wuka har lahira a Mararaba dake jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: