Wajibi ne APC ta lashe zabe a 2023 saboda ban taba rashin nasara ba, Abdullahi Adamu
- Sabon Shugaban jam'iyya mai mulki ya bayyana dalilin da yasa ya zama wajibi APC ta lashe zabe a 2023
- Abdullahi Adamu yace irin namijin kokarin da Shugaba Buhari ya yiwa Najerya na basu tabbacin nasara
- Sanata Abdullahi Adamu tsohon gwamnan jihar Nasarawa ne kuma ya kwashe sama da shekaru 10 a majalisa
Abuja - Shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Sanata Abdullahi Adamu ya lashi takobin tabbatar da cewa jam'iyyarsa ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Abdullahi Adamu, wanda tsohon Gwamna ne kuma Sanata, ya ce bai taba rashin nasara a wani abu da ya jagoranta ba kuma a wannan ma ba zai fadi ba.
Adamu ya bayyana hakan karshen makon da ya gabata a hira da manema labarai a gidansa na Abuja, rahoton Informationng.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace ko kadan ba zasu yarda su fadi ba saboda wannan ne aikinsu na farko kuma abinda zasu yi shine dakatar da duk wani abinda zai sa suyi rashin nasara, riwayar DailyTrust.
Yace:
"Na gode Allah a rayuwata kawo yanzu, daga gwagwarmayar siyasa lokacin ina dalibi har wa yau, ban taba rashin nasara ba, ban taba fadi ba. Idan akwai matsala, ina kokarin gyarawa."
"Amma abinda ke kara bani kwarin gwiwa shine shugaban kasa ya yi aiki sosai kuma wajibi ne mu tabbatar ya sauka daga mulki cikin farin ciki."
"Ba mu da wani zabi, zamu yi nasara. Abinda zamuyi kenan."
Gwamna Buni ya miƙa ragamar jam'iyyar APC hannun sabon shugaba na ƙasa
Sabon shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya karbi jagorancin jam'iyya ta ƙasa daga hannun shugaban riko.
Shugaban kwamitin rikon kwarya da shirya babban taro kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya damƙa ragamar APC a hannun Adamu a hukumance.
Hakan ya kawo ƙarshen tsawon watanni 21 da Buni ya jagoranci APC tun bayan naɗa shi shugaban kwamitin riko.
Taron miƙa ragamar jagorancin jam'iyya ya gudana ne a babban ɗakin taro na kwamitin NWC dake Sakatariyar APC ta ƙasa a babban birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng