Wahalar fetur za ta zama tarihi, Lai ya nuna yadda matatar Dangote za ta taimaki Najeriya

Wahalar fetur za ta zama tarihi, Lai ya nuna yadda matatar Dangote za ta taimaki Najeriya

  • Ministan yada labarai da al’adu na kasa ya ganewa kan sa irin aikin da Dangote ya ke yi a Legas
  • Alhaji Aliko Dangote yana gina matatar da za ta rika tace gangunan danyen mai 650, 000 a duk rana
  • Da zarar wannan aiki ya kammala a shekarar nan, jama’a za su daina wahalar bin layin shan mai

Lagos - Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Lai Mohammed ya tabbatar da cewa matatar man Dangote za ta kawo karshen wahalar man fetur a Najeriya.

The Cable ta ce Alhaji Lai Mohammed ya yi wannan bayanin ne da ya kai ziyara zuwa matatar da attajirin nahiyar yake ginawa a Ibeju, Lekki da ke jihar Legas.

Wannan kamfani da matata da za su ci Dala biliyan 19 wajen ginawa za su iya tace ganguna 650, 000 na danyen mai duk rana. Hakan zai taimakawa kasar nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Amaechi Ya Shiga Jerin Masu Son Ɗare Wa Kujerar Buhari a 2023

“Mun kewaya mun ga daya daga cikin katafororin kwangilolin da ake yi a yau a duk Duniya, Dangote Refinery and Petrochemical Plant.”
“Kafin nan, mun ziyarci kamfanin takin Dangote. Daga nan, za a iya cewa Dangote yana jagorantar juyin juya-halin masana’antu a Najeriya.”
“Wannan matata ta $19bn za ta canza yadda abubuwa ke tafiya wajen samar da ayyukan yi, kuma za ta taimaka wajen samar da kaya a gida.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matatar Dangote
Matar Dangote a Legas Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC
“Sannan za ta taimaka wajen adana kudin kasar waje domin ba za a rika shigo da mai daga ketare ba, kuma a samu kudin shiga daga ketare”
“Matatar za ta tabbatar da samuwar kayan mai, hakan zai jawo a daina layin shan man fetur, a kuma kudin kwadaito kamfanonin kasar waje.”

- cewar Alhaji Lai Mohammed

Hukumar dillacin labarai ta rahoto Mohammed yana cewa idan an gama kwangilar a karshen shekarar nan, za a samu isasshen mai, kuma abinci zai wadata.

Kara karanta wannan

Amaechi: Dama na yi hasashen za a kawo hari a jirgi, na nemi kayan tsaro amma aka hana

Gwamnati ta taimaka - Devakumar Edwin

Solacebase ta ce babban darektan wannan aiki na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ya yabawa gwamnati kan gudumuwar da su ka bada wajen yin aikin.

Devakumar Edwin ya ce za su rika samar da duk wani man fetur, dizil, kananziri da man jirgin sama da ake bukata, har kuma a fitar da 40% zuwa kasashen waje.

Za a gama gina gadar 2nd Niger

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta bayyana abin da ta kashe a aikin gina babbar gadar Neja-Delta. Zuwa yanzu an batar da N157bn domin ginin gadar ‘Second Niger’.

Ku da labari cewa hukumar Nigerian Sovereign Investment Authority ce ta ba kamfanin Julius Berger Nigeria Plc aikin gina gadar ‘Second Niger’ a yankin Neja-Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng