Da Duminsa: 'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Hari a Kaduna, Ana Fargabar Sun Kashe Mutane Da Dama

Da Duminsa: 'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Hari a Kaduna, Ana Fargabar Sun Kashe Mutane Da Dama

  • Wasu miyagu da ake zargin yan bindiga ne sun kai hari a unguwar Sabon Tasha da ke karamar hukumar Chikun a Kaduna
  • Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan masu dimbin yawa sun afka unguwar ne a daren ranar Alhamis suka kuma bude wa mutane wuta
  • Ana fargabar mutane da dama sun mutu sakamakon harin duk da cewa dai kawo yanzu rundunar yan sanda bata ce komai game da harin ba

Kaduna - Ana fargabar mutane da dama sun mutu sakamakon harin da yan bindiga suka sake kai wa a wani gari a karamar hukumar Chikun na Jihar Kaduna.

TVC News ta rahoto cewa yan ta'addan masu dimbin yawa sun afka Anguwan Bulus da ke Sabon Tasha misalin karfe 10 na daren ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: IBB ya gana da 'yan takarar shugaban kasa 4 daga yankin Arewa

Da Duminsa: 'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Hari a Kaduna, Ana Fargabar Sun Kashe Mutane Da Dama
Yan ta'adda sun afka Sabon Tasha a Kaduna, Ana Fargabar Sun Kashe Mutane Da Dama. Hoto: The Nation.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da cewa rundunar yan sandan Jihar Kaduna bata riga ta tabbatar da kai harin ba, an fahimci cewa yan ta'addan sun bude wa mutane wuta a garin.

Ana fargabar cewa an kashe mutane da dama, wasu da dama sun fice daga gidajensu a cikin daren.

Wannan sabon harin yana zuwa ne kwanaki hudu bayan wasu yan ta'addan sun saka bam a jirgin kasa inda a kalla mutane takwas suka rasu, wasu da dama suka jikkata.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164