An sake samun matsala, an rasa rai yayin da wani jirgin kasa ya samu hadari a Kaduna

An sake samun matsala, an rasa rai yayin da wani jirgin kasa ya samu hadari a Kaduna

  • Jirgin kasan da yake zuwa Legas daga garin Kano ya yi hadarin da ya jawo asarar rai a Kaduna
  • Hukumar NRC ta tabbatar da cewa wannan jirgi ya goce ne bayan ya yi lodin lemu zai kai Kano
  • An bayyana cewa direban jirgin ya mutu, kuma har zuwa yanzu ba a san inda gawarsa ta shiga ba

Kaduna - An samu labarin wani hadarin jirgin kasa bayan jirgin da ya taso daga garin Legas zuwa Kano ya goce a daidai Farin Ruwa a jihar Kaduna.

Wannan gari na Farin Ruwa ya na kusa ne da garin Jaji ne a karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Jaridar Vanguard a rahoton da ta fitar a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris 2022, ta ce hukumar NRC ta kasa ta tabbatar da wannan labari a Zaria.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ga 'yan Najeriya: Ku tarawa 'yan uwanku talakawa da harin jirgi ya shafa kudin magani

Mai magana da yawun bakin NTC na shiyyar Arewacin Najerya, Abdullahi Alhaji ya shaidawa hukumar dillacin labarai na kasa abin da ya faru jiya.

Direba ya rasu

Abdullahi Alhaji ya bayyana cewa direban wannan jirgi, Bala Kawu ya mutu a lokacin da wannan mummunan abin ya auku da jirgin da ya dauko kaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami’in ya ce jirgin ya na dauke da lemu ne da za a kai garin Kano a lokacin da ya goce daga layinsa a dalilin sace karafunan dogon da wasu suka yi.

Jirgin kasa
Wani jirgin kasa Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Mutane su na bi, su na sace shimfidar dogon, hakan ta sa ya jirkice yayin da ake cikin tafiya a titi.

A jawabin na sa, Abdullahi Alhaji ya ce jami’an NRC su na neman gawar direban jirgin kafin a iya karasa wannan tafiya da aka yi niyya zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Amaechi: Dama na yi hasashen za a kawo hari a jirgi, na nemi kayan tsaro amma aka hana

Wannan jirgin ya na daukar kaya da jama’a ne tun daga Legas zuwa jihar Kano, ya na bi ta Kaduna inda a nan ne ya gamu da wannan hadarin.

An tare jirgin Kaduna-Abuja

Hakan na zuwa ne 'yan kwanaki kadan bayan 'yan bindiga sun tare jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna. Wannan abin ya faru ne a daf da garin Rijana.

Matafiya da-dama sun mutu, yayin da wasu kuma su ka fada hannun masu satar mutane.

Mohammed Bazoum ya shiga Aso Villa

A daidai wannan lokaci ne aka ji shugaban kasar Nijar, Mohammed Bazoum ya godewa shugaba Muhammadu Buhari a kan aikin jirgin da za a kai Maradi.

Rahotanni sun ce za a kashe Dala biliyan $1.96 wajen wannan aiki da zai taso daga Kano zuwa Katsina, sai ya tike a garin Maradi da ke jamhuriyyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng