Kwamishinan Albarkatun Ruwa Na Jihar Kano Ya Ajiye Aikinsa

Kwamishinan Albarkatun Ruwa Na Jihar Kano Ya Ajiye Aikinsa

  • Kwamishinan ma’adanan ruwa na Jihar Kano, Sadiq Wali ya yi murabus daga kujerarsa a ranar Alhamis sannan ya yi godiya ga Gwamna Ganduje
  • Ya bayyana hakan ne ta wata takarda wacce ya saki, i da ya ce ya yi hakan ne domin bunkasa harkokinsa na siyasa
  • An gano cewa Wali yana shirin tsayawa takarar gwamnan Jihar Kano ne sannan an san cewa shi dan jam’iyyar PDP ne, hakan ya sa ya saki kujerarsa

Jihar Kano - A ranar Alhamis, kwamishinan ma’adanan ruwa na Jihar Kano, Sadiq Wali ya yi murabus daga kujerarsa, Daily Nigerian ta ruwaito.

A wata takarda wacce ya sanya wa hannu kuma Daily Nigerian ta gani, Wali wanda dan jam’iyyar PDP ne ya mika godiyarsa ga Gwamna Abdullahi Ganduje akan ba shi damar yi wa jiharsa hidima.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kwamishina ya yi murabus daga muƙaminsa, ya sayi Fam ɗin takara a PDP

Kwamishinan Albarkatun Ruwa Na Jihar Kano Ya Yi Murabus
Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Sadiq, Na Jihar Kano Ya Yi Murabus. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

A cewarsa, ya yanke shawarar yin murabus din ne don ya samu damar ci gaba da kujiba-kujibarsa ta siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishinan Albarkatun Ruwa Na Jihar Kano Ya Ajiye Aikinsa
Takardar murabus na Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Kano.
Asali: Twitter

Shekarunsa biyu yana kan kujerar kwamishina

Kamar yadda ya ce:

“Na yi matukar farin cikin samun damar yin aiki da gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma mutanen kirkin Jihar Kano a matsayin kwamishina kuma daya daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na tsawon shekaru biyun da suka gabata.
“Yau na yanke shawarar ci gaba da harkar siyasa hakan yasa nake sanar da batun murabus dina a matsayina na kwamishinan ma’adanan ruwa a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris din shekarar 2022.”

Wali dan tsohon ministan harkokin kasashen waje ne, Aminu Wali, kuma ya yaba wa kokarin Ganduje na gyara akan harkar ruwan jihar.

An gano cewa yana shirin takarar gwamna ne

Kamar yadda ya shaida:

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Okorocha ya ce ya kamata Tinubu ya hakura ya bar masa tikitin APC

“Gwamnatin nan ta yi iyakar kokarinta na ganin ta kawo gyara don bunkasa harkar ruwa a jihar ta hanyar samar da wadataccen ruwa kuma ta hakan noman rani ya bunkasa.”

Ya tabbatar wa gwamna Ganduje batunsa na kasancewa na hannun damansa sannan mai mara masa baya daga yanzu har nan gaba, idan kuma akwai bukatar taimakonsa a shirye yake da ya bayar.

Kuma ya ce ya ji dadin yadda ya yi aiki da gwamnatin Ganduje. Ya yi masa fatan alheri da kuma samun damar kammala shugabancinsa lafiya.

Daily Nigerian ta gano cewa Wali yana shirin tsayawa takarar gwamnan jihar ne a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: