Maza gudunmu suke, ba su neman aurenmu, Mata nakasassu sun koka da rashin mazan aure

Maza gudunmu suke, ba su neman aurenmu, Mata nakasassu sun koka da rashin mazan aure

  • Shugabar kungiyar haɗakan nakasassu ta ƙasa ta koka a kan yadda nakasassu ke rasa mashinshina musamman a Najeriya
  • Ann Ujugo ta ƙara da bayyana yadda maza har da nakasassu suka zaɓi barin su gwauraye har ƙarshen rayuwarsu ba tare da yi masu tayin aure ba
  • Babu wani kokari da gwamnati ke yi wajen kawo ƙarshen wariya da kyarar da suke fuskanta a cikin al'umma, musamman dokar hakin yara, wacce a halin yanzu bata aiki

Shugabar ƙungiyar haɗakar nakasassu ta ƙasa (JONAPWD) na jihar Edo, Ms Ann Ujugo, ta koka game da yadda a Najeriya nakasassun mata ke fuskantar wariya, idan aka zo batun aure.

Ta ce, mazan Najeriya basa aurensu, suna barinsu a gwauraye tsawon rayuwarsu, Leadership ta ruwaito.

Maza gudunmu suke, ba su neman aurenmu, Mata nakasassu sun koka da rashin mazan aure
Maza gudunmu suke, ba su neman aurenmu, Mata nakasassu sun koka da rashin mazan aure. Hoto daga bbc.com
Asali: UGC

Ojugo ta fadi hakan ne jiya a Benin City, jihar Edo, yayin zantawa da manema labarai don tunawa da ranar mata ta duniya a ranar 8 ga watan Maris na kowacce shekara.

Kara karanta wannan

Abun Kunya: Wani Magidanci ya ɗirka wa ɗiyarsa ciki har sau biyu, ya saki Matarsa ta Sunnah

Ta ce, ƙalubalen da muke fuskanta ya haɗa da rashin aikin yi, wariya a makarantu da kasuwanni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta, "Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da nakasassun mata suke fuskanta shine wariya a batun aure, saboda babu namijin, koda kuwa nakasashshe ne, baya zuwa neman auren mu.
"Wasu kan tambayemu idan muna jin yadda mata ke ji. Domin wariya ga mace mai nakasa ƙarin wani ƙalubale ne garemu. Ilimi wani ƙalubale ne, wasu mutane basa son tura yaransu mata makaranta, balle kuma a yi magana a kan mutum mai nakasa."

A jawabinta na farko, Miss Janet Omole, wata mamban JONAPWD, ta ce, ranar farinciki ce garesu, saboda rana ce da suka zaɓa ranar mata da yara mata masu nakasa, don ɗaga muryarsu tare da sauran matan Najeriya, sannan su godewa matsayin mata ga al'umma, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Magidanci ya lakada wa tsohuwar matarsa da sirikarsa mugun duka a kan 'ya'yansu

"Babban abunda aka daɗe ana jaddadawa cikin haƙkokin mata a shekaru sama da 30 da suka shuɗe shine, kawo daidaito tsakanin maza da mata a makarantu, wuraren aiki, da sauran wurare, wanda akawa samfoti cikin cigaba marasa yankewa guda 5.

Sai dai, a al'ummar Najeriya, rashin wakilai, rashin isashshen ilimi, kyara a cikin al'umma, wariya a wajen aiki, cin zarafi ko neman yin lalata dasu, na daga cikin manyan ƙalubalen da nakasassun mata da yara mata ke fuskanta a halin yanzu.

"Mata da yara masu nakasa na cigaba da fuskantar wariya a cikin jama'a da al'ada tare da sauran matsaloli a cikin al'umma. Gwamnati na nuna halin ko in kula kan shawo kan matsalolin ba tare da amfani da dokar adalci kamar dokar hakkin yara, wacce bata aiki saboda rashin tsayayyar soka," a cewarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng