'Yan Fashi Sun Kutsa Gidan Shugaban HEDA, Sun Sace Motarsa Da Wasu Kayayyaki Masu Muhimmanci
- A ranar Litinin, ‘yan fashi sun kai farmaki gidan shugaban cibiyar habaka al’umma da muhalli, HEDA, Olanrewaju Suraju, inda suka sace mota da sauran tsadaddun abubuwa
- Cikin abubuwan da suka sace akwai waya kirar Samsung, da wayoyi iPhone guda biyu, iPad guda biyu, na’urori masu kwakwalwa, sarkoki da ‘yan kunnaye, katinan banki da sauransu
- Sakataren HEDA, Sulaiman Arigbabu ya bayyana hakan a ranar Talata inda ya ce sun kai farmakin ne gidan Suraju da misalin karfe 2:15 na asuban ranar Litinin inda ya ce sun je da bindigogi da wukake
Legas - ‘Yan fashi da makamai sun kai farmaki gidan shugaban cibiyar habaka al’umma da muhalli, HEDA, Olanrewaju Suraju inda suka sace wata mota kirar Toyoto Corolla 2014 da sauran abubuwa masu tsada, The Punch ta ruwaito.
Cikin abubuwan da suka sace akwai waya kirar Samsung, iPhone guda biyu, iPad guda biyu, na’urori masu kwakwalwa na Macbook guda biyu, da wata na’urar mai kwakwalwa daban, katinan banki da yawa, makullan motoci, takardun ofis da sauransu.

Kara karanta wannan
Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Source: Twitter
Sakataren HEDA, Sulaimon Arigbabu, ya bayyana hakan ta wata takarda wacce ya saki ranar Talata inda ya ce ‘yan fashin sun shiga gidan Suraju da misalin karfe 2:15 na asubar ranar Litinin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sun yi yunkurin halaka shugaban HEDA din
Ya bayyana yadda ‘yan fashin suka shiga gidan da bindigogi, wukake da sauran miyagun makamai suna yunkurin halaka Suraju.
Arigbabu ya ce sun ci zarafin shugaban HEDA da matarsa wadanda yanzu haka suke kwance a asibiti ana kulawa da laifiyarsu.
A cewarsa, kamar yadda The Punch ta nuna, kamarar CCTV ta fara daukar ‘yan ta’addan wadanda ganin haka yasa suka lalata ta da miyagun makamansu.
Yanzu haka dai ba za a iya fadin takamaiman abubuwan da suka lalata ko suka sace ba, kamar yadda Arigbabu ya shaida.
Cikin gidaje 220 da ke rukunin gidajen, gidan Surajo kadai suka shiga
Ya ci gaba da cewa:
“Yan fashin sun kai farmaki gidan Suraju duk da cewa gidaje 220 ne a rukunin gidajen, kuma sun amshe tsadaddun abubuwa a gidan sannan sun titsiye shi sai da ya ba su bayanai dangane da wayarshi da na’urori masu kwakwalwar da suka amshe a hannunshi da sauransu.
“Sannan tun farko sai da suka goge duk wani bidiyon da CCTV din ta dauka sannan suka umarci iyalansa su kashe na’urar.”
Yanzu haka an sanar da ofishin ‘yan sandan na Jihar Legas wanda ya kamata halin da ake ciki.
Ya kwatanta lamarin a matsayin abu mai ban tsoro kuma yanzu haka ana zargin har da aikin HEDA na kawo cikas ga rashawa ya janyo suka kai wa Suraju harin
Asali: Legit.ng
