Najeriya na kara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali kullum, Gwamnatin Buhari

Najeriya na kara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali kullum, Gwamnatin Buhari

  • Gwamnatin tarayya tace kowace rana Najeriya na ƙara samun aminci da zaman lafiya ta kowane ɓangare
  • Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ce jami'an tsaron Najeriya sun nuna jajircewa, sun cancanci yabo
  • Ministan ya yi bayanin yadda gwamnatin tarayya ta taimaka wa jami'an tsaro da kayan aiki har ake samun nasara

Abuja - Gwamnatin tarayya tace Najeriya na samun zaman lafiya da aminci kowace rana tare da nasarori a yaƙin da take da Boko Haram/ISWAP, yan bindiga da sauran ayyukan ta'addanci.

Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ne ya faɗi haka a wurin taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Alhaji Lai Muhammed.
Najeriya na kara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali kullum, Gwamnatin Buhari Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace dakarun tsaro a Najeriya sun zafafa yaƙi da yan bindiga kuma suka jefa su cikin halin gudun ɓuya yayin da kullum ake ƙara tarwatsa sansanonin su.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ma'aikatan jami'a karkashin SSANU da NASU sun hargitsa jami'ar Legas

Tribune ta rahoto A jawabinsa ya ce:

"Ina alfahari da jami'an tsaron mu maza da mata dake cin ɗamara, duk da taɓarɓarewar ƙalubalen tsaro, ba su karaya ba kuma sun jajirce."
"A dai-dai lokacin da suka tarwatsa yan ta'addaa sansanonin su, wasu dubbanni tare da iyalansu na miƙa wuya tare da aje makamai."
"Hukumomin tsaro sun tsaya da digadigan su ne bisa jagorancin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ke samar musu da kuma sadaukarwan jami'an tsaro da shugabannin su."

Yadda FG ta samar da kayan aiki

Muhammed ya bayyana cewa sama da sojoji 1,500 aka ɗauka aiki a rundunar sojin ruwa cikin shekarar nan yayin da sojojin sama (NAF) suka karɓi sabbin jiragen yaƙin Super Tucano 12 da JF-17 Thunder Fighter guda uku.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Tsagin hamayya na kulla-kullan ruguza Najeriya' Gwamnatin Buhari ta fallasa sirrin

Ya ce dakarun sojin sun yi amfani da jiragen wajen luguden wuta ta sama, taimakawa sojin ƙasa, da kuma lalata sansanonin yan bindiga da makamansu.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kai mummunan hari wata Hedkwatar yan sanda a Imo, mutane yankin sun tsorata sun yi takan su

Mazauna ƙauyen sun shaida wa manema labarai cewa maharan sun shigo da karfe 3:00 na dare, kuma sun kwashe dogon lokaci yayin harin.

Wani mazaunin yankin ya ce Artabun da aka yi tsakankin dakarun yan sanda da maharan ya hargitsa mutane kamar duniya ce zata tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel