Da duminsa: Sojoji da ke sintiri a Sambisa sun samo ragowar jirgin NAF da yayi hatsari a 2021
1 - tsawon mintuna
- Rundunar sojin kasan Najeriya ta gano ragowar jirgin saman NAF da ya bace watanni 11 da suka shuɗe
- Jirgin ya ɓace ne yayin da rundunar ke hanyar kaiwa sojin ƙasan Najeriya ɗauki a jihar Borno a shekarar da ta gabata
- Yayin sanar da cigaban, rundunar ta sanar da yadda ta gano ragowar jirgin a lokacin da take sintiri a dajin Sambisa cikin Borno
Sambisa, Borno - Dakarun sojin kasan Najeriya na rundunar kakkabo hamada sun gano ragowar jirgin saman sojin saman Najeriya(NAF) da ya ɓace watanni 11 da suka shuɗe.
Rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter kan yadda jirgin saman Alpha Jet (NAF475) ya ɓace, yayin da yake kan hanyarshi ta kai gudunmawa ga sojin kasan Najeriya a Borno.
A lokacin, matuƙan jirgin har mutum biyu ne ke cikin jirgin.
Yayin bayyana cigaban a ranar Asabar, dakarun sojin sun bayyana yadda rundunar ta samu ragowar yayin da rundunar ke sintiri a dajin Sambisa a jihar Borno.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Asali: Legit.ng
Tags: